Ƴan Nijeriya Sun Biya Diyyar Naira Bilyan 4 Ga Masu Garkuwa Da Mutane A shekaru 4

 

A cikin shekaru hudu Gwamnatin Nijeriya da sauran ƴan ƙasa sun biya sama da Naira Billiyan hudu ga masu garkuwa da mutane a matsayin kuɗin fansa.

Wani rahoto ya yi nuni da cewa, ‘’tsakanin watan Yuni na 2011 zuwa ƙarshen Maris na 2020, bayanan da muka samu ya nuna cewa tsakanin Yunin 2011 zuwa ƙarshen Maris 2020, an biya Dala Miliyan 18.34 a matsayin kudin fansa na karɓo mutane a hannun masu garkuwa’’.
 A wani rohoton kuma da muka samu daga cibiyar tattara bayanan sirri ta SBM, masu kula da matsalolin garkuwa da mutane da bada kuɗaɗen fansa a Nijeriya, ya yi nuni da cewa, ‘’har ila yau, abu mafi tsoratarwa a cikin wannan al’amari shi ne, kaso mai yawa na wannan adadi (na ƙusan Dala Miliyan 11) an biya shi ne tsakanin watan Janairun 2016 zuwa Maris 2020, wanda ke nuna cewa garkuwa da mutane ya fi kowane laifi yawa a kasar nan.
Rohoton ya kuma ƙunshi dukkan Jihohin Nijeriya 36, da kuma babban birnin tarayya, Abuja. Rohoton ya ce, 18 daga cikin Jihohin, akwai, Akwa Ibom, Anambra, Borno, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Kano, Kwara, Legas, Nasarawa, Ogun, Ondo, Osun, Plateau, Ribas, Taraba da Jihar Yobe, wanda a kowane yunƙurin satar mutum sai an yi kisa.
Ganduje ya Wai wayi Taran Kano da aka sace
Jihar Ribas, a cewar rohoton ta fi kowace jiha samun yawaitar satar mutane, domin an saci mutane sama da 120 tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, sai kuma jihar Kaduna da ke da 117. Delta ita ce ta uku, tare da mutane 96 da aka sace. Bayelsa ita ce ta hudu da laifuka 85, sai Borno ta biyar da laifuka 82.
Akwai kuma sauran manyan Jihohi 10 da abin ya yawaita sosai kamar, Kogi da ke da mutane 59 da ka sace, sannan Jihar Edo tana da 55, Ondo 54, Katsina 52, da Taraba mutane 47.
Rohoton ya ci gaba da cewa, yawaitar garkuwa da mutane zai iya haifar da tashe-tashen hankula a Jihohin.
Ina barci Mata ta yanke min Azzakari
Rahoton ya ce, ƙarshen maganar mu shi ne, a duk inda yawan aikata laifuka yayi yawa, za a iya rasa rayukan mutane, kuma zai iya haifar da yawaitar manyan laifuka kamar, fyaɗe, garkuwa da mutane da dai sauran su’’.
Bayelsa, Jihar Kudu maso Kudu, rahoton ya nuna cewa, ita ce kadai Jihar da take da koma-baya a wasu ayyukan ta, saboda matsalar garkuwa da mutane, idan aka kwatanta da shekarar 2011-2015 lokacin ta bunkasa. 
Kaduna, Ribers, Katsina, Zamfara da Taraba, sune akafi samun yawaitar laifin garkuwa da mutane, a cewar rahoton.
Rahoton ya yi bayanin cewa, wani babban tarihin tashin hankali yana Kaduna, musamman akan hanyar zuwa Abuja, shi ya sa Kaduna ta kasance ta biyu a yawan garkuwa da mutane a Nijeriya.
Duk da cewa ba a sa babban birnin tarayya Abuja a cikin manyan Jihohi 10 da ke da matsalar satar mutane a Nijeriya ba, rahoton ya ce ‘’akwai ƙwararan hujjoji wanda ke nuna Abuja za ta iya zama ta biyu a Jihohi masu matsalar satar mutane a Nijeriya. Domin a can ne masu garkuwa da mutane na Jihar Kaduna ke shirya aikin su.
Rahoton ya ƙare da cewa, duk da cewa sace-sacen na iya zama akai-akai, masu garkuwa da mutanen suna zaɓar wanda suka san cewa za su samu kudi a jikinsa ne, domin sun mayar da laifin tamkar sana’a, suna yin shi akai-akai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.