Ganduje ya ƙaddamar da kwamitin zartar da rahoton hanyoyin shawo kan matsalar sace yara

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya ƙaddamar da kwamitin zartar da rahoton hanyoyin shawo kam matsalar sace yara da akeyi wanda a kwanakin baya aka kama wasu ƴan kudu wanda suka daɗe suna wannan mummunan aiki. 

Gwamnatin jiha tare da hukumar ƴan sanda sun yi nasarar samo wasu daga cikin yaran wanda aka maida su hannun iyayen su.
Sakamakon wannan ne Gwamna Ganduje ya ga dacewar kafa wannan kwamitin domin ganin cewa irin wannan bata sake faruwa ba a Kano ba.
Kwamitin na ƙarƙashin Jagorancin Mai Shari’ah Wada Umar Rano, sannan yana da membobi da suka hada da wakilin hukumar yan sanda, da na jami’an tsaro na farin kaya, da na shige da fice, da hukumar yaki da safaran mutane musamman yara da kungjyar malamai, wato Council of Ulama da kuma Shugaban Kungjyar Kiristoci reshen jihar Kano da sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.