Ina barci Mata ta yanke min Azzakari

Ranar Talata, 30 ga Yuni, 2020, wata rana ce da Aliyu Umaru, ba zai taba mantawa ba a rayuwarsa saboda a wannan rana uwargidarsa, Halima, ta guntule masa azzakari da wuka. 

Yanzu Yana kwance a asibiti cikin raɗaɗin jiki da damuwa a zuciya a asibitin koyarwar gwamnatin tarayya dake Gombe, inda aka kaisa bayan aukuwan lamarin.
 A asibitin, an ga yadda Likitoci suka sanya masa na’ura na musamman domin taimaka masa wajen yin fitsari yayinda aka ajiye azzakarinsa da matar ta yanke gefe guda cikin leda. 
A hirar da jaridar Punch tayi dashi, Aliyu Umar ya bayyana irin iftila’in da ya shiga ciki. 

Yace: “Ni dillalin Likitocin dabbobi ne. Ina sayar da magungunan dabbobi. 
Shekaru na 42 kuma ina da mata biyu da yara biyu.” “Ni mazaunin garin Tella ne a karamar hukumar Gassol a jihar Taraba. 
An turo ni asibitin koyarwa na tarayya na Gombe daga FMC Taraba.”
 “Bayan dawowa na daga aiki, na debi ruwa don yin wanka kuma na ci abincin da iyalina ta girka kuma nayi bacci. 
Daga baya wani mugun azaba ya tasheni daga barci ina ihu.” “Uwargidata ta yanke min ‘Azzakari’. 
A lokacin ne aka sanar da makwabta. Ban sani ba (akwai yiwuwan) an sanya magani cikin abincin saboda yadda nayi bacci mai zurfi.
 Matata ta lalata min rayuwa kuma akwai takaici.” 
Rahotanni sun nuna cewa Halima ta kasance cikin takun saƙa da mijinta da kishiyarta. 
Ɗan’uwan Umaru, Malam Usman ya bayyana cewa yana gidansa cikin dare aka kirashi a waya cewa akwai matsala.
 Yace: “Cikin dare wayata ta fara kara, ya yana Ya faɗa min abinda ya faru da shi. 
Da wuri aka garzaya da shi FMC Taraba domin tsayar da jinin dake kwarara da kuma yi masa tiyata.”
 “Amma suka kasa yin aikin saboda sun ce basu da isasshen kayan aiki. 
Sai suka bamu shawaran kai shi wani asibitin na daban.” 
“Ita kuma mun faɗawa mutane kada wanda ya taɓa ta. 
Aikin gama ya gama kuma babu yadda zamuyi. Mun barta da Allah. Babu abinda zamuyi mata da zai dawo da azzakarin ‘dan uwana.” 

Leave a Reply

Your email address will not be published.