An gayyaci Ibrahim Magu, shugaban EFCC fadar shugaban ƙasa amsa tambayoyi

An gayyaci Ibrahim Magu, shugaban EFCC  fadar shugaban ƙasa amsa tambayoyi
  An gayyaci muƙaddashin shugaban hukumar yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon kasa, (EFCC) gaban kwamiti don bayani a kan ayyukan hukumar. 
An gano cewa, kwamitin na wannan zaman ne a Banquet Hall da ke fadar shugaban kasa. 
An tsare Magu a cunkoson motoci da ke wucewa zuwa anguwar Wuse II na EFCC a Abuja kuma aka mika masa goron wannan gayyatar. 
Duk da Magu na kan hanyarsa ta zuwa hedkwata, ya roki jami’in da ya tsaresa a kan ya bar sa inda daga baya sai ya amsa wannan gayyatar. 
Amma kuma an sanar da shi cewa gayyatar wannan kwamitin ta fi muhimmanci.
 Wurin karfe 1:35 na rana, Ibrahim Magu ya isa fadar shugaban kasa inda aka shigar da shi inda zai yi bayanan.
 A wannan lokacin, lauyan Magu, Rotimi Oyedepo, ya samesa a fadar shugaban kasar. 
Wata majiya ta ce: “Magu da Jacob a halin yanzu suna wani ofishin da ke fadar shugaban kasar. 
“Ba a kama shi ba, kuma babu wata hukumar tsaro da ta damke shi. 
Muna sauraron ci gaban da zai faru a gaba.” Karin bayani na nan tafe… 
SERAP ta bawa buhari wa’adin mako biyu kan ɓatan Bilyan 300

Leave a Reply

Your email address will not be published.