An kama Faston da yayi shekara 5 Yana lalata da yarinya

An yi ram da wani Faston da ya yi shekara da shekaru yana lalata da yarinyar gida

Fasto Joseph Alhassan na cocin Faith Agape Church a Narayi, jihar Kaduna, ya shiga hannun jami’an tsaro bisa zargin cewa ya dade yana lalata da wata yarinya ‘yar shekara 16.
Jami’an hukumar NSCDC na reshen jihar Kaduna sun damke Joseph Alhassan ne a gidansa da ke kan titin Abdulrahman a unguwar Barnawa da ke garin Kaduna.
Hukumar ta yi nasarar cafke wannan Bawan Allah bayan ma’aikatar kula da jama’a da walwalar al’umma a jihar Kaduna ta kai kararsa gaban jami’an tsaro a ranar Asabar.
Ina barci Mata ta yanke min Azzakari
A yayin da wata jami’ar gwamnati, Brenda Bartholomew, tayi hira da ƴan jarida, ta ce wanda ake zargi watau Joseph Alhassan ya shafe shekaru biyar yana tarawa da wannan yarinya.
Brenda Bartholomew take cewa wannan Fasto ya yi ta amfani da yarinyar ne ba tare da amincewar ta ba. An yi wannan ne a lokacin da yarinyar take aiki a matsayin boyi-boyinsa.
Ainihin wannan yarinya, mutuniyar garin Saminka ce, a karamar hukumar Lere, kuma tun tana ‘yar shekara 11 take zama da malamin addinin kamar yadda NAN ta rawaito
Ƴan Najeriya sun biya diyyar Bilyan 4 ga masu garkuwa da mutane
Hukumar dillacin labarai ta ƙasa watau NAN ta ce kungiyar Bridge that Gap Initiative ce ta fara kawo kukan wannan mutumin, wanda hakan ya janwo gwamnatin Kaduna ta binciki lamarin.
“Bayan mun samu bayani, mun kai maganar gaban ofishin hukumar NSCDC da ke karamar hukumar Kaduna ta kudu, a Kakuri.” Inji jami’ar ma’aikatar kula da jama’a da walwalar al’ummar.
Misi Bartholomew ta cigaba da cewa: “Bayan nan ne dakarun NSCDC suka kama Alhassan, kuma yanzu ana binciken lamarin.”
Bisa dukkan alamu nan gaba kadan za a gurfanar da wannan malamin coci a gaban kotu domin amsa laifin da ke kansa.
“Mun kai ita (wanda ake zargin an yi amfani da ita) zuwa cibiyar kula da wadanda aka yi wa fyade a Kakuri, domin a duba lafiyarta, a yayin da muke jiran NSCDC su kammala bincikensu, kafin mu yi gaba, mu shigar da kara a kotu.”

Anyi ram da mahaifin da yayi wa ƴarsa ciki

Leave a Reply

Your email address will not be published.