An Rushe Shagunan Siyar da giya da gidajen Baɗala a Sabon Garin Kaduna

AN RUSHE MANYA DA ƘANANUN SHAGUNAN SIYAR DA GIYA DA SAURAN GIDAJEN BADALA A FADIN KARAMAR HUKUMAR SABON GARIN JAHAR KADUNA

A kokarin gwamnatin karamar hukumar Sabon Garin Kaduna na tsaftace rayuwar al’ummarta, ta fuskar hana sayar da giya da sauran miyagun kwayoyi da kuma gidajen baɗala.
A ranar Asabar 4th July 2020, Gwamnatin ƙaramar hukumar Sabon Gari, karkashin shugaban karamar hukumar Alaramma, Injiniya Muhammad Usman, ta samu nasarar rushe shaguna 21 masu lambobi kamar haka;
L17    L18     L25   L29   L30  L33   L34   L35
L36    L37     L38   L39   L40  L41   L45   L46
L54    L55     L56   L57   L58
Wadanda suke a IBB Road dake PZ Sabon Gari Zaria.
Duk da kungiyar masu sayar da giyan sun shigar da Gwamnatin karamar hukumar ta Sabon Garin Ƙara a kotu, kuma ana kan shari’ar a yanzu haka.
Haka kuma gwamnatin ta rushe waɗannan shaguna ne domin shagunan suna a matsayin mallaki tane.
Anyi Ram da Faston da ya shekarar 5 Yana lalata da yarinya
Sannan kuma bisa la’akari da korafe-korafen da Al’umma suke shigarwa na lalata tarbiyya da kasancewar wajen matattarar masu aikata miyagun laifuka da kuma barazanar rashin zaman lafiya da shagunan ke haddasawa;
Gwamnati ta hana sana’ar sayar da giya a wajen kwata kwata.
Daga ƙarshe kuma gwamnatin Karamar Hukumar ta Sabon Gari tana jan hankalin al’ummar dake zaune a IBB Road dama Al’ummar Karamar Hukumar Sabon Gari baki dayan su, su kwantar da hankalin su, kuma su kasance masu bin doka da oda, musamman a wannan lokaci da ta daura damarar yaki da guraren aikata fasadi a fadin karamar hukumar baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.