DSS sun hana ƴan jarida shiga inda ake tuhumar Magu a fadar Shugaban ƙasa

 

DSS sun hana ƴan jarida shiga inda ake tuhumar Magu a fadar Shugaban ƙasa

– Jami’an hukumar tsaro na farin kaya, sun hana manema labarai shiga dakin taron da shugaban hukumar yaƙi da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu ke amsa tambayoyi
– A yau Litinin ne dai labarin damke Magu ya bayyana inda aka zargin hukumar DSS da aikata kamun nasa.
– Manema labaran fadar shugaban kasa sun gangara dakin taron da shugaban EFCC yake don tabbatar da lamarin amma jami’an DSS suka fatattake su.
Sai dai kuma jami’an DSS wadanda ke danƙare a farfajiyar domin taron sun umarci manema labarai da su bar wurin, jaridar The Nation ta ruwaito.
“Sun ce ku haƙura da amfani da wannan wurin na yau,” wani jami’in su ya sanar da manema labarai cike da tausasa murya.
SERAP ta bawa buhari wa’adin mako biyu kan ɓatan Bilyan 300
An gano cewa, kwamitin na wannan zaman ne a Banquet Hall da ke fadar shugaban kasa.
An tsare Magu a cunkoson motoci da ke wucewa zuwa anguwar Wuse II na EFCC a Abuja kuma aka mika masa goron wannan gayyatar.
Duk da Magu na kan hanyarsa ta zuwa hedkwata, ya roki jami’in da ya tsaresa a kan ya bar sa inda daga baya sai ya amsa wannan gayyatar. Amma kuma an sanar da shi cewa gayyatar wannan kwamitin ta fi muhimmanci.
Wurin karfe 1:35 na rana, Ibrahim Magu ya isa fadar shugaban kasa inda aka shigar da shi inda zai yi bayanan.
A wannan lokacin, lauyan Magu, Rotimi Oyedepo, ya samesa a fadar shugaban kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.