DSS ta yi karin haske a kan kama Ibrahim Magu

Babu hannunmu’: DSS ta yi karin haske a kan kama Ibrahim Magu 

 Hukumar jami’an tsaro na farin kaya (DSS) ta ce ba ta kama muƙaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ba. 
A cikin wata sanarwa da jami’an hulda da jama’a, Peter Afunanya, DSS ta ce babu gaskiya a cikin labarin da wasu kafafen yada labarai ke yaɗawa a kan cewa ta kama Magu.
 “Hukumar DSS ta na son sanar da jama’a cewa ba ta kama Ibrahim Magu, muƙaddashin shugaban hukumar EFFC ba, kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka bayyana ba.
 “DSS ta fitar da wannan sanarwa ne a yau, Litinin, 6 ga watan Yuli, bayan yawan tuntubarta a kan zargin kama Magu,” a cewar sanarwar. 
SERAP ta bawa buhari wa’adin mako biyu kan ɓatan Bilyan 300

Leave a Reply

Your email address will not be published.