FG ta sanar da ranar fara jarabawa WAEC a Najeriya

FG ta sanar da ranar fara jarrabawar WAEC a Najeriya

– Hukumar jarrabawa ta WAEC ta sanar da ranar fara jarrabawar masu kammala sakandire na shekarar 2020
– Za ayi jarabawar tsakanin 4 ga watan Augusta zuwa 5 Satumban 2020
– Ƙaramin ministan ilimi, Emeka Nwajuiba ne ya sanar da hakan a yayin taron kwamitin yaki da cutar korona na ƙasa
Wannan sanarwar ta zo ne a yayin bayanin da kwamitin yaƙi da cutar korona na fadar shugaban kasa (PTF) ƙarƙashin shugabancin Boss Mustapha, ke yi a Abuja.
SERAP ta bawa buhari wa’adin mako biyu kan ɓatan Bilyan 300
A gefe guda, mun ji a baya cewa gwamnatin jihar Kano ta yi magana dangane da jita-jitar da ke yaɗuwa a tsakanin al’umma na cewa a yau Litinin, 6 ga watan Yuli, za a bude makarantu ga wani rukuni na dalibai.
Legit.ng ta fahimci cewa, wasu daga cikin rukunin daliban da gwamnatin tarayya ta ba da umarnin a bude musu makarantu, sun shirya abinsu sun tafi makarantu da safiyar yau ta Litinin.
Sai dai fa sun riski makarantun a rufe, lamarin da ya sa a dole suka dawo gida ba bu shiri kuma ba tare da sun yi farin ciki a kan lamarin ba.
A yayin da ‘yan kwanakin nan al’umma jihar Kano sukayi ta rade-radin za a bude makarantu a yau Litinin, wani gargadi da gwamnatin jihar tayi ya disasashe duk wani tsammaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.