SERAP Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin sati biyu kan ɓatan Naira Bilyan 300

SERAP Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin sati biyu kan ɓatan Naira Bilyan 300

 Ƙungiyar kare haƙƙiin tattalin arziƙi mai zaman kanta ta SERAP ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da ya umurci babban Lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN, da kuma sauran hukumomin hana cin hanci da karɓar rashawa da su binciki zargin da ake yi kan ɓatan wasu kuɗaɗen al’umma da jimillansu ya kai naira Biliyan 300 
Ƙungiyar ta ce kuɗaɗen an shigar da su a rahoton da babban Lauyan na gwamnatin tarayya ya fitar na shekarar 2017, amma ko dai an yi sama da faɗi da kuɗaɗen ne ko kuma an karkatar da su ta wani wajen a hanyar sata.
FG ta sanar da ranar Zana jarabawar WAEC a Najeriya
SERAP ta bai wa gwamnatin tarayyan wa’adin kwanaki 14 da ta umurci babban Lauyan gwamnatin tarayya da kuma sauran hukumomin hana cin hanci da karɓar rashawa da su binciko inda kuɗaɗen suka shiga, kuɗaɗen waɗanda ake ta raɗe-raɗin an yi almundaha ne da su ko kuma facaka a ma’aikatun gwamnatin tarayya da sauran hukumomin gwamnatin.
 Ƙungiyar ta ce, “Muna buƙatar a ɗauki matakin da ya dace a cikin kwanaki 14 da wallafa wannan sanarwar tamu, matukar an gaza yin hakan, SERAP ba ta da wani zaɓi face ta nufi kotu, inda za ta maka gwamnatin a gaban masu shari’a domin binciko inda dukiyar al’umma ta saƙale.
Ƙungiyar ta SERAP ta kuma aike da kwafin wasiƙar zuwa ga babban Lauyan gwamnatin tarayya Malami, da shugaban hukumar nan ta hana cin ganci da karban rashawa ta ICPC, Farfesa Bolaji Owasonaye, da shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, da Ministar Kudi da kasafin kuɗi kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed.
Wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 4 ga watan Yuli, 2020, wacce kuma mataimakin daraktan kungiyar ta SERAP, Kolawole Oluwadare, ya sanya mata hannu, kungiyar ta ce rahoton na shekarar ta 2017 ya nuna a fili zargin yin almundahana da kuma karkatar da dukiyar al’umma ta hanyar sata gami da wasu kasha-kashen kudaden da sam ba a bayar da wani bahasi a kansu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.