Akwai Yi wuwar A Sake Rufe Nijeriya saboda ƙaruwar masu kamuwa da korona -cewar PTF

Akwai Yi wuwar A Sake Rufe Nijeriya, Baki Daya Bayan Gwamnoni Uku Sun Sake Kamuwa Da korona, Cewar Gwamnatin Tarayya

A ranar Litinin ne kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa domin yaƙi da annobar cutar COVID-19 yayi magana game da ƙaruwar masu ɗauke da cutar Coronavirus a Najeriya.
Kwamitin ya koka kan cewa cutar na ƙara yawa a ƙasar, wanda hakan yana tasiri kai-tsaye wajen sha’anin gudanar da mulki da kuma harkar tsaro.
Shugaban PTF kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana wannan a lokacin da suka zanta da manema labarai jiya a babban birnin tarayya Abuja.
Boss Mustapha yake cewa baza ayi watsi da yi wuwar sake kawo sabuwar dokar hana fita ba, muddin an samu bukatar yin hakan domin a kare lafiya da ran al’umma.
Mustapha ya ja-kunnen mutane su rika bin dokokin da malaman lafiya suka gindaya, domin a cewarsa babu ruwan wannan cuta da matsayin mutum.
SERAP ta bawa buhari wa’adin mako biyu kan ɓatan Bilyan 300
Jaridar Vanguard ta ce wannan gargaɗi da gwamnati tayi ya zo ne a daidai lokacin da gwamnoni uku suka kamu da muguwar cutar a cikin makon da ya gabata.
COVID-19 ta harbi David Umahi na Ebonyi, Ifeanyi Okowa na Delta da takwaransa na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, wanda shi tuni ya warke.
A kwanakin bayan nan mun samu ƙaruwar waɗanda ke dauke da kwayar cutar COVID-19, musamman a cikin manyan mutane masu mulki.” Inji Boss Mustapha.
Wannan yana da tasiri kai-tsaye ga gudanar da mulki da tsaron kasarmu. Mu na kira ga gaba ɗayan mutane su ƙara ta-ka-tsan-tsan. Wannan kwayar cuta ba ta kula da mukamin mutum.
Ya ce: “Idan abin ya yi ƙamari, in ta kama za mu bada shawarar a rufe gari. Za mu fadawa shugaban kasa, shi zai duba lamarin, ya ɗauki mataki bayan shawarar da muka bada.
Shugaban wannan kwamiti ya ce PTF za su cigaba da aika sakonni domin wayar da kan jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published.