An hana waƙoƙin yabon Annabi a Kano sai da izinin gwamnati cewar Afakallah

An hana waƙoƙin yabon Annabi a Kano sai da izinin gwamnati -cewar Afakallah

“Tuni muka nemi gidajen rediyo a Kano su daina sanya irin wadannan wakoki har sai lokacin da muka bayar da izini” inji Afakallah
Hukumar tace fina-fanai da sauran adabi ta jihar Kano ta ce babu wani sha’iri da zai kara waka a jihar sai idan ta ba shi lasisi ba.
Shugaban hukumar Isma’il Muhammad Na’abba wanda aka fi sani da Afakallah ne ya bayyana hakan a wata hira da BBC tayi da shi.
Afakallah ya ce ganin yadda sha’irai ke wuce iyaka a lokuta da dama yasa hukumar ta dauki wannan azama.
Ya kuma ce ko an bai wa sha’iri lasisi idan ya yi wakar sai ya kawo an saurara an tabbatar da babu wani abu na ɓatanci a ciki.
Isma’il Muhammad Na’abba ya ce an kafa wannan hukuma ne kan abu uku kan harkokin addini cikin abubuwan adadi, da al’adu da kuma zamantakewa ta yadda kowa zai girmama addini da al’adar abokin zamansa.
Ya zuwa yanzu in ji Afakallah ya ce akwai wakoki uku zuwa biyar da suka taɓa rikita jihar Kano sakamakon rashin tantancewa.
“A baya mun ba su damar tace wakokin da suke yi ta hanyar jagorancin wasu shugabanninsu amma sai abin yazo da rikici shi yasa a yanzu muka dawo da ragamar aikin hannunmu.
”Abin yana ci mana tuwo a kwarya ganin ganin yadda ake shiga hurumin Allah da Annabinsa, da kuma yadda ake zagin manyan bayin Allah duk da sunan yabo,” in ji Afakallah.
Shugaban ya ce mutanen jihar Kano masu riko da addini ne don haka suka fara yunƙurin ɗaukar mataki da kansu a baya kan irin waɗannan abubuwa, don haka gwamnati ta farga kuma da sannu za a yi wa tufƙar hanci.
Za a riƙa bai wa irin waɗannan mawaka horo domin sanin me suke waƙewa da kuma kalaman da ya kamata su rika amfani da su
Afakallahu ya ce “Tuni muka nemi gidajen rediyo a Kano su daina sanya irin waɗannan waƙoƙi har sai lokacin da muka bayar da izini”.
Da aka tambaye shi ganin cewa ba su da adadin mawakan da ke jihar sai ya ce: “A ko wacce karamar hukuma muna da ofishi kuma ko wanne ofishi da kayan aikin da za a iya aikin tace waƙa a cikinsa don haka ba abu ba ne da zai ba mu wuya wajen shawo kansa.
Mun tanadi hukunce-hukuncen da za mu yi wa duk wanda ya karya dokar da aka shimfiɗa, domin mu tabbatar da ya zama izina ga ‘yan baya.”
Za a rika bai wa irin waɗannan mawaka horo domin sanin me suke waƙewa da kuma kalaman da ya kamata su rika amfani da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.