Duk Wanda YaYi Wakar Yabo Ba Tare Da Iznin Hukumar Tace Finafinai Ba, Zai Fuskanci Hukunci- Ismaila Afakallahu

Duk Wanda YaYi Wakar Yabo Ba Tare Da Iznin Hukumar Tace Finafinai Ba, Zai Fuskanci Hukunci- Ismaila Afakallahu

Hukamar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano ta ce daga yanzu duk wani mai wakar yabon Fiyayen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W) sai ya nemi izinin hukumar kafin sakin waka ko gudanar da majalasi a Jihar Kano.
Shugaban hukumar, Isama’ila Na Abba Afakallah ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan kammala taro da gamayyar mata masu yabo da ya gudana a ofishin hukumar a jiya.
Afakallahu ya ce sun dauki matakin ne la’akari da irin abubuwan dake faruwa a wasu lokutan da ma su yabo ke gudanarwa a majalasi ko yabo wanda ya sa hukumar ke kokarin magance abubuwan da suka sabawa doka.
Ya ce wannan dalilin ya sa :muka yanke hukunci daga yanzu duk maison yayi yabon Annabi ko Majalisi sai mun bashi izini”.

Leave a Reply

Your email address will not be published.