Majalisar Wakilai ta Umarci INEC ta mayar Naira Bilyan 73 daga kuɗin Zaɓen 2015

 

Majalisar Wakilai ta buƙaci INEC ta mayar da rarar N73bn da ta karɓa 

 Kwamitin majalisar wakilai ya buƙaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta mayar da rarar biliyan N73 da ake zargin ta karɓa lokacin zaɓen shekarar 2015. 
Kwamitin, mai kula da yadda ake kashe kuɗaɗen jama’a, ya yi zargin cewa INEC ta karɓi rarar biliyan N73 daga ofishin babban akanta na ƙasa (AGF) bayan biliyan N45 da aka fara bawa hukumar domin gudanar da zaɓen 2015.
 Shugaban kwamitin, Wole Oke, da sauran mambobinsa sun kafe a kan cewa sai hukumar INEC ta mayar da rarar kudaden asusun gwamnati. 
Ɗaliban Najeriya ba za su rubuta jarabawar WAEC  ba a 202
 
Kwamitin ya zargi ofsishin AGF da karya ka’ida wajen kasafta kudaden gwamnati sabanin ikon da ya ke da shi. 
‘Yan majalisar sun bukaci ofishin AGF ya mayar da rarar wata biliyan N16.9 daga cikin biliyan N36.9 da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin a bawa INEC amma sai iya biliyan N10 ofsihin AGF ya bawa hukumar.
 A cewar shugaban kwamitin, warewa INEC biliyan N107.7 da kuma kara mata wata biliyan N73 sabanin biliyan N45 da aka fara amincewa da bawa hukumar daidai yake da sabawa doka, wanda bai kamata ofishin AGF ya aikata hakan ba. 
Majalisar dattawa ta mayar da wa’adin sefetan ƴan sanda shakara 4

Leave a Reply

Your email address will not be published.