Haramun ne Albashin da ƴan Majalisu ke karɓa -Cewar Shugabar Ma’aikatan Najeriya

Gwamnati ta ce albashin da Ma’aikatan Majalisa su ke karba haramun ne saboda karya doka

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Folasade Yemi-Esan, ta ce akwai matsala a game da tsarin albashin CONLESS na ma’aikatan gwamnati na majalisar tarayya.
Misis Folasade Yemi-Esan ta bayyana cewa yadda ake aiki da tsarin CONLESS ya sabawa doka.
Jaridar The Cable ta fahimci cewa shugabar ma’aikatan gwamnatin ta yi wannan jawabi ne a lokacin da ta gana da shugabannin majalisar tarayya a garin Abuja.
Folasade Yemi-Esan ta zauna da shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila da kuma takwaransa na majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan.
An Kama hatsabibin ɗan ƙungiyar Asiri
Rahoton da mu ka samu ya ce Yemi-Esan ta bukaci Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila su maida albashin ma’aikatan na majalisun a kan tsarin da suke kai a can baya.
A ‘yan shekarun baya an samu wasu ma’aikatan gwamnati da ke aiki da majalisa wanda suka rika kukan cewa ba su san albashi mai tsoka, wannan yasa aka kara masu kudi.
MAJALISA Ta buƙaci INEC Ta mayar da Naira Bilyan 73
Bukola Saraki ne ya jagoranci wannan canji da aka samu a albashin ma’aikatan gwamnatin a lokacin da ya ke rike da kujerar shugaban majalisar dattawa a Najeriya.
A yanzu kuma shugabar ma’aikatan gwamnati ta kasa ta fadawa ‘yan majalisar cewa akwai wasu kura-kurai da aka samu wajen dabbaka wannan sabon tsarin albashi.
A cewar Folasade Yemi-Esan, ma’aikatan gwamnati da ke aiki a majalisa ba su da bambanci da sauran ma’aikatan gwamnatin tarayya da ke wasu ma’aikatu a fadin kasar nan.
Bayan cewa ma’aikatan ba su bukatar a ba su wani albashi na dabam, Yemi-Esan ta ce akwai matakai da ake bi a ka’idar gwamnati kafin a kawo sabon tsarin albashi.
Akwai ma’aikatan gwamnati na musamman wadanda su ke aiki da bangaren ‘yan majalisa. Sai da ta kai wadanan ma’aikata sun yi zanga-zanga domin ganin sun samu kari a albashinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.