Manyan Abubuwa 5 da suka faru da Ibrahim Magu cikin kwanaki 4

Manyan Abubuwa 5 da suka faru da Ibrahim Magu cikin kwanaki 4 

Cikin ƴan kwanaki hudu da suka gabata daga ranar Litnin 6 ga watan Yuli, 2020 zuwa yau Alhamis, 9 ga Yuli, 2020, muhimman abubuwa 5 sun faru da shirin yaƙi da cin hanci da rashawa na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari. 
A lokutan yaƙin neman zaɓe na shekarar 2015 da 2019, shugaba Muhammadu Buhari bai gushe ba, yana jaddada cewa yaki da cin hanci da rashawa na cikin abubuwa uku mafi muhimmanci da zai yi. 
Amma da alamun wanda ya naɗa don wanzar masa da wannan manufa na cikin halin ƙaƙa-nikayi kuma yaƙi da rashawar na fuskantar barazana. 
Kawo yanzu, ba’a san takamammen wanda aka nada domin rikon kwaryar shugabancin hukumar hana yaƙi da rashawa da yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa EFCC ba. 
Osinbajo ya musanta karɓar biliyoyin naira daga wurin dakataccen shugaban EFCC
Legit ta tattaro muku jerin abubuwa 5 da suka faru da dakataccen shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, cikin kwanaki hudu. 

1. An kamashi ranar Litinin
 A ranar Litinin, wasu jami’an tsaro sanye da farin kaya sun tsare Ibrahim Magu yayinda yake kokarin zuwa ofishin sifeton yan sanda IG Mohammed Adamu. 
Sun tare shi a bakin kofa kuma sukayi awon gaba dashi zuwa fadar shugaban kasa.

 2. Ya gurfana gaban kwamitin bincike na musamman karkashin Alkali Ayo Isa Salami Yayinda jami’an tsaron suka dira da shi fadar shugaban kasa.
 Magu ya gurfana a gaban kwamiti na musamman da shugaba Muhammadu Buhari ya nada domin yi masa tambayoyi. 
Kwamitin karkashin jagorancin tsohon shugaban kotun kolin Najeriya, Alkali Ayo Isah Salami, yana da hakkin yi masa tambayoyi kan wasu tuhume-tuhume da ake zarginsa. 
Binciken Magu: Osinbajo ya rubuta takardar korafi zuwa ofishin IGP
3. A tsareshi a ofishin yan sanda
Da misalin karfe 10:15 na dare bayan kwamitin binciken fadar shugaban ya kammala yiwa Ibrahim Magu tambayoyi, jami’an yan sandan sun yi awon gaba da shi ne daga fadar shugaban kasa.
 An dakatar da dogaransa kafin a tafi da shi.
 The Nation ta samu labarin cewa bayan zaman tambayoyin da akayi masa, an shigar da Magu wata motar fara kirar Hilux mai lamba 37ID. Amma Magu ya ce sam ba zai shiga ciki ba, sai dai ya zauna a bayan motar. 
Daga baya yan sandan suka shawo kansa ya shiga cikin motar. Daga karshe dai aka garzaya dashi ofishin binciken hukumar yan sanda FCID cikin motarsa.
 4. An dakatar da shi daga kujerarsa 
A ranar Talata, labari ya fito daga fadar shugaban kasa cewa: shugaba Buhari ya dakatar da Ibrahim Magu daga matsayin mukaddashin shugaban hukumar EFCC. 

5. An Kai simame tare da bincike a gidajensa 
Wasu jami’an ‘yan sanda da ke aiki da sashen binciken manyan laifuka (FCIID) sun binkice gidan Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC da shugaba Buhari ya dakatar. 
Wani babban jami’in dan sanda ya tabbatarwa da jaridar ‘Punch’ cewa an gudanar da bincike a gidan Magu da ke kan titin Abduljalil a unguwar Karu da ke wajen birnin tarayya, Abuja. 
Babban jami’in ya bayyana cewa sun kwashe wasu muhimman takardu daga gidan Magu bayan sun shafe sa’o’i su na gudanar da bincike 

Leave a Reply

Your email address will not be published.