An hana ƴan Najeriya neman aiki a Dubai

An hana ƴan Najeriya neman aiki a Dubai

Ƴan Najeriya na bayyana fushinsu a shafukan sada zumunta bayan da aka wallafa wani tallan neman ma’aikata a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, wanda a ciki aka fito ƙarara ana cewa ba a buƙatar ƴan Najeriya su nemi aikin.
Tallan da kamfanin Shirley Recruitment Consultants ya wallafa a shafinsa na intanet ya sanar da masu neman aiki cewa ana neman wadanda za su iya aikin tallan turare ne a Dubai, kuma ana bukatar su kasance masu kwarewa kan harkar kasuwanci na a kalla shekara uku.
Tallan ya kuma ce “ƴan Afirka maza ko mata na iya neman aikin amma ban da ƴan Najeriya.”
Magu ya nemi beli a wurin Sifeton ƴan sanda

Wani dan Najeriya da ya soki tallan a dandalin sada zumunta na Twitter: ya ce “Hana ƴan Najeriya kawai su nemi aiki da wata kasa ta yi, nuna bambanci ne kuma ya taka dokokin kasa-da-kasa.”

Wasu ƴan Najeriya da suka yi tsokaci kan batun a shafukan sada zumunta na da ra’ayi cewa kamun da aka yi wa wasu ƴan Najeriya masu damfarar mutane da a halin yanzu suna hannun hukumomin Amurka na da nasaba da wannan matakin da kamfanin ya dauka.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.