Magu ya nemi beli a wurin Sifeton ƴan sanda

Magu ya nemi beli a wurin Sifeton ƴan sanda

  Dakatattacen muƙadashin shugaban yaƙi da rashawa ta EFCC, Mr Ibrahim Magu da ake bincika a kan zargin rashawa, ya nemi Sufeta Janar na Rundunar Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya bayar da shi beli. 
Kwamiti na musamman da shugaban kasa ya kafa, karkashin jagorancin tsohon alkalin kotun koli Ayo Salami ne ke bincikar Magu.
 Magu, wanda aka tsare tun ranar Litinin ya rubuta wasiƙa ta hannun lauyansa, Mr Oluwatsosin Ojaomo a ranar Juma’a zuwa ga IG na neman beli kamar yadda The Punch ta ruwaito. 
OSINBAJO YA SHIGAR DA KARA KAN YI MASA ƘAZAFIN YA ƘARƁI BILYAN 4
Tun ranar da aka kama shi, Magu yana tsare ne a wani wurin ajiya na rundunar ‘yan sanda a Abuja inda daga nan yake zuwa gurfana gaban kwamitin binciken. 
Wasikar da lauyansa ya rubuta zuwa ga ofishin IGP mai dauke da kwanan wata na 10 ga watan Yuli kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito ta nemi a bayar da shi beli, “bisa sanayar da aka masa a kasa.” 

Leave a Reply

Your email address will not be published.