Kwamitin Shugaban ƙasa ya ban kaɗo Naira Bilyan 5,50 da EFCC ta ƙwato

Yadda aka kwashe ruwan N550bn da EFCC ta kwato

Kwamitin fadar shugaban ƙasa na bayani a kan kadarorin da aka dawo da su a Hukumar yaki da rashawa karkashin dakataccen mukaddashin shugaban hukumar, Ibrahim Magu.
Kwamitin na binciken kadarorin gwamnati da EFCC ta kwato daga watan Mayun 2015 zuwa Mayun 2020.
Kwamitin ya sanar da cewa an kwashe rarar da aka samu a kan kuɗi har Naira Bilyan 550 da aka samu a karkashin shugabancin Magu, kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito.
Kwamitin ya ce an kasa bada bayani a kan rarar samar kudin da aka samu.
“Akwai matukar damuwa a kan yadda ake yada labarai daban-daban a kan yawan kudin da aka samo yayin kwato dukiyar gwamnati,” rahoton yace.
“Akwai abubuwa mabanbanta a kan sahihancin rahoton da EFCC ta fitar. 
Kwamitin ya gano cewa EFCC ba za ta iya bada takamaiman yawan kudin da ta samo ba.
“A yayin da EFCC ta ruwaito cewa ta samo N504,154, 184, 744. 04, abinda ke asusun bankin ya kai N543, 511, 792, 863. 47. Wannan lamarin ya nuna kenan akwai kudi har N39,357, 608, 119.43 fiye da yadda ta ruwaito.
“Dole ne a ce banbancin naira biliyan 39 da aka samu baya hade da ruwan kudin da ake zubawa a asusun bankin tun bayan budesa.
“Hakan ce ta saka kokwanto mai yawa a kan sahihancin yawan kudin. Rashin bayyana kudin ke nuna cewa ana kwasheshi tun bayan da aka saka N550 biliyan din a asusun.
“Wannan bayyanannen al’amari ne na yadda hukumar yaki da rashawar ta cika da rashawa.”
Kwamitin ya sake bayyana yadda NFIU ta bankado wasu al’amuran rashawa da handamar dukiyar kasa wacce wasu jami’an EFCC ke yi har da Magu.
“NFIU ta bada rahoton yadda mukaddashin shugaban EFCC ke amfani da salo kala-kala wurin kwasar kudi a wasu lokutan har da karbar cin hanci daga wadanda ake zargi,” rahoton ya kara da cewa.
A baya mun ji cewa kwamitin fadar shugaban kasa a kan bayanin kadarorin da aka samo (PCARA) ya ce Ibrahim Magu, yayi amfani wani malamin addini wajen watanda da kuɗaɗe a ƙasashen ketare.
A halin yanzu, ana tuhumar Magu a gaban wani kwamiti wanda yake ƙarƙashin shugabancin Ayo Salami, tsohon shugaban kotun ɗaukaka ƙara.

Leave a Reply

Your email address will not be published.