Gwamnatin Kano ta ware Bilyan 3 Domin yaƙar cutar Maleriya

A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya kaddamar da shirin bayar da tallafi ga mata masu juna biyu da kuma kananan yara.

Haka kuma Ganduje ya kaddamar da shirin yi wa kananan yaran da ba su wuce watanni uku zuwa shekaru biyar da haihuwa ba allurar rigakafin zazzaɓin cizon sauro.

Ganduje ya ce gwamnatinsa tare da hadɗin gwiwar kungiyar Malaria Consortium, ta ware naira biliyan 3 da za ta batar domin tabbatar da nasarar wannan shiri da ta ƙaddamar.

Furucin gwamnan ya zo ne a ranar Lahadi yayin da yake kaddamar da shirin a karamar hukumar Bichi da ke shiyyar Kano ta Tsakiya.

Ganduje yayin jaddada ɗaura ɗamarar da yayi, ya ce yawaitar matsalar zazzaɓin cizon sauro musamman a wannan lokaci na damuna, ita ta sanya gwamnatinsa ta miƙe tsaye domin tunkarar lamarin.

Ya ce gwamnatinsa ta karkatar akalart hankalin ta tare da bayar da fifiko a kan rigakafin cutar zazzabin cizon sauro da sauran cututtukan da ke kassara yara.

Kamar yadda Gidan Talibijin na kasa NTA ya ruwaito, Ganduje ya sake jaddada muhimmancin da gwamnatinsa ta bai wa lafiyar mata masu juna biyu da kuma kananan yara, lamarin da yake jan hankalin iyaye a kan basu haɗin kai.

Ganduje ya lura da yadda duniya ta ruɗu tare da mayar da hankali a kan daƙile yaɗuwar annobar korona, ya ce ita kuwa gwamnatinsa ta ɗaura ɗamarar tunkarar wasu cututtukan na daban.

Ya kara da cewa, gwamnatinsa ta bullo da ingantattun shirye-shiryen na bunkasa harkar kiwon lafiya da ke mai da hankali kan sauran cututtuka.

A nasa jawaban, kwamishinan lafiya na jihar Dr. Aminu Tsanyawa, ya ce wannan shiri da gwamnatin ta kaddamar zai yadu a dukkanin kananan hukumomi 44 da ke fadin Kano.

Dakta Tsanyawa ya yi bayanin cewa, za a rika gudanar da wannan shiri cikin kwanaki hudu na kowane wata tun daga watan Yuli har zuwa Oktoban shekarar da muke ciki.

Ya kara da cewa, gwamnatinsa ta bullo da ingantattun shirye-shiryen bunkasa harkar kiwon lafiya da mai da hankali kan sauran cututtuka.

A nasa jawaban, kwamishinan lafiya na jihar Dr. Aminu Tsanyawa, ya ce wannan shiri da gwamnatin ta kaddamar zai yadu a dukkanin kananan hukumomi 44 da ke fadin Kano.

Dakta Tsanyawa ya yi bayanin cewa, za a rika gudanar da wannan shiri cikin kwanaki hudu na kowane wata tun daga watan Yuli har zuwa Oktoban shekarar da muke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published.