Anyi binciken ƙwa-ƙwaf a Offishin Magu tare da awon Gaba da Na’urar Bayanai

Yadda Ma’aikata su ka bincike ofishin Magu tsaf, sukayi gaba da wata muhimmiyar na’ura

A ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2020, aka tura wasu masu bincike da suka tsefe ofishin shugaban hukumar EFCC da aka dakatar watau Ibrahim Magu.
Jaridar The Nation ta ce an lalube ofishin Ibrahim Magu ne a sakamakon binciken da kwamitin Ayo Salami yake yi a kan tsohon shugaban hukumar ta EFCC.
Rahotan ya fahimci cewa an dauki wata na’ura mai kwakwalwa daga ofishin shugaban hukumar. Ana tunanin za a samu muhimman bayanai a cikin wannan na’ura.

Magu ya Yi barazanar daina Cin Abinci sakamakon tsare shi

https://www.arewagist.com.ng/2020/07/magu-ya-bayyana-matakin-da-zai-dauka.html

Bayan haka kuma masu binciken sun taso wasu manyan jami’an EFCC a gaba da tambayoyi jiya.
Majiyar hukumar ta fadawa jaridar cewa: “Masu binciken sun lalube ofishin, sannan suka tafi da wata babbar na’ura da ake zargin akwai bayanai a cikinta.”
“An bukaci wasu manyan mukarraban Magu su bayyana a gaban kwamitin binciken domin suyi wasu ƙarin bayanai. Suna wurin har kusan karfe 9:30 na dare.”
Bayan an laluba ofishin na Magu, an kuma tsare wasu manyan hadimansa. Jaridar The Nation ta ce an yi wa mukarraban tsohon shugaban hukumar tambayoyi a jiya.
Daga cikin waɗanda aka rutsa a binciken akwai wani muƙaddashin darektan harkokin karɓe dukiyar sata na hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin zagon-ƙasa.
An karɓe wayoyin wasu daga cikin waɗannan hadimai inda aka binciki wasu bayanai. A ƙarshe an ƙyale su sun tafi gida bayan dare ya tsala.
    An sake Zargin Magu Kan ɓatan dabon Kadarori 332 
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/an-sake-zargin-mukaddashin-shugaban.html

Ana tunanin cewa kwamitin ya na neman karin bayani ne a game da wasu kadarori 332 da hukumar EFCC ta karɓe daga hannun barayi a karkashin Ibrahim Magu.
Majiyar ta ce: “Ina tunanin cewa an buƙaci ganin Aliyu Yusuf ne a game da wasu kadarori da aka karɓe daga hannun waɗanda ake tuhuma da satar dukiyar gwamnati.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.