Mutum miliyan 690 ne ke fama da yunwa a faɗin duniya’

Mutum miliyan 690 ne ke fama da yunwa a faɗin duniya’

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum miliyan 690 ne ke fama da yunwa a fadin duniya, kimanin kashi 9 cikin 100 na yawan mutanen duniya.

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ne ya bayyaa hakan a shafinsa na tuwita, yana cewa wasu karin mutane ka iya kara tsintar kansu cikin halin yunwar a wannan shekarar.

“Dole mu samar da tsarin abinci mai dorewa tare da kara lafiya wanda kowa zai iya samu a ko ina.”

Masana na ganin halin da duniya ta tsinci kanta a ciki na da alaka da annobar korona da ta mamaye kusan ko ina a duniya.

Sabbin mutane miliyan 71 za su shiga ƙangin talauci  -cewar MDD
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/sabbin-mutane-miliyan-71-za-su-shiga.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.