An kashe mijimmu an bar mana marayu 15 a Batsari

An kashe mijimmu  an bar mana marayu 15 a Batsari’

Daya daga cikin matan da aka kashewa mazajensu a yankin Batsari na Katsina a Najeriya ta bayyana wa BBC irin mawuyacin halin da suka shiga tun bayan da ‘yan bindiga suka kashe maigidansu.

Matar ta ce su uku ne mijinsu ya bari da kuma ‘ya’ya 15, kuma a yanzu haka suna samun mafaka a cikin garin Batsari inda suke fafutukar abin da za suci su da yaransu

Matar ta ce Babban ɗansu shekarar sa 14 ƙaramin shekara 1

Ta ƙara da cewa mijinsu yana cikin gida, ƴan bindigar suna ta harbe-harbe cikin gari, sai mijin na su ya tsare domin ya tsira da ransa, ashe ƴan bindigar sun ganshi yana ta gudu, suka bishi suka kashe shi.

Yaran mu ada, suna makaranta amma yanzu ba suyi, saboda halin da aka shiga.

Muna zaune a gidan haya, inda mun samu a biya shi kuɗin dubu saba’in da biyar 75,000

Wani lokacin muna samun taimakon dangi, sannan wataran yaran suna samun taimakon abinci a waje, idan basu samo ba, su dawo gida suyi ta kuka.

Wani lokacin maƙota idan suka jiwo kukan yaran, sukan taimaka da tuwo ko kwaki ko abinci sai mu gyara mu basu.

Idan mun sami ɗan kaɗan sai mu ƙara da ruwa, muyi hauri, mu barwa yaran masu kuka.

Sau biyu muke iya samun abinci da safe da kuma magariba, sai kuma wata safiyar, amma ba ma ƙoshi gaskiya. inji matar

Kafin a kashe mai gidammu, yana ba mu abinci kai da kai, sau uku a rana, kuma yana yin noma.

Ba musan inda ƴan uwan mai gidan mu suke ba, duk an tar watsa mu, wasu ƴan uwan mu suna jibiya, wasu kuma batsari, wasu ma ba musan inda suke ba, amma suna cikin batsari, saboda an tar watsa kowa ba musan inda dangi suke ba.

Abin babu daɗi, in kaga abin sai ka tausaya.

Idan mun sami kwanciyar hankali za mu ci gaba da yin sana’a, in mun sami damar yi, saboda ada, muna sana’a lokacin kwanciyar hankali.

Tun da farko a hirar da BBC ta fara yi da Sarkin Ruman Katsina, Hakimin Batsari Alhaji Tukur Mu’azu Ruma ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe fiye ɗaru-ruwan magidanta a karamar hukumarsa tare da barin zawarawa fiye da 600 da marayu fiye da 2000.

Sannan ya ce kusan kashi daya cikin uku na mutanen masarautarsa sun zama ‘yan gudun hijira inda suka warwatsu a jihohi makwabta da sauran sassan Najeriya.

Basaraken ya ce yankinsa na cikin wani matsanancin hali na matukar bukatar agajin gwamnati da masu hannu da shuni, duk da ya ce gwamnati na ciyar da mutanen da ke gudun hijira a wani sansani.

Leave a Reply

Your email address will not be published.