An saki Magu bayan tsare shi na Kwanaki goma

An saki Magu bayan tsare shi na Kwana goma

An sako dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu bayan ya shefe kwana 10 a tsare yana fusknatar bincike.

A ranar Litinin 6 ga watan Yuli ne Jami’an tsaro na DSS suka kai Magu gaban kwamitin da Shugaban Kasa ya kafa domin binciken zarge-zargen da ake masa guda 12 kan jagorancinsa a EFCC.

Tuhume-tuhumen sun hada da kasa bayar da bayani kan kudin ruwan da aka samu a kan kuɗi Naira biliyan 550 da aka kwato daga wasu barayin dukiyar gwamnati.

Yana fuskantar bincike ne a gaban kwamitin tsohon Mai Shari’a Ayo Salama, lamarin da ya sa aka dakatar da shi tare da daukacin darektoci da wasu manyan jami’an gudanarwan hukumar.

Za A Riƙa Dandaƙe Masu Fyaɗe A Kano https://www.arewagist.com.ng/2020/07/za-rika-dandae-masu-fyade-kano.html?m=1

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.