Buhari ya Bada Umarnin ci Gaba da ɗaukar Ma’aikata 774,000

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa ministan kwadago da Ma’aikata na ƙasa, Festus Keyamo, damar ci gaba da daukar ma’aikata 774,000 a karkashin shirin gwamnati na Ayyukan Jama’a na Musamman (SPW).

Keyamo ne ya tabbatar da bayyana cigaba da aikin a ranar Talata a Abuja. 
Ministan ya ce, ya sami umarnin Shugaba Buhari game da ci gaba da aikin ba tare da wata damuwa ba, ta hanyar yin watsi da umarnin Majalisar kasa wacce ta nemi Ministan ya dakatar da shirin.
“Ina da umarnin shugaba na, Shugaban kasa, ya ce in cigaba” Keyamo ya faɗi hakan.
Ministan da ‘yan majalisun dai sun kasance cikin saɓani game da batun aiwatar da shirin daukar ma’aikatan 774,000.

Mutum miliyan 690 ne ke fama da yunwa a faɗin duniya’

Yan majalisar sun ce, Ministan bai nemi bayanan suba tun da farko, har ya kaddamar da kwamiti mai mutum ashirin a watan Yuni da za su gudanar da zaɓin mutanan da za’a ɗauka a kowacce jiha.
Sun zargi Ministan da kokarin kwace ragamar aikin daga Hukumar Kula da Aiki ta Kasa (NDE).
Sai dai Keyamo wanda ya bayyana agaban kwamitin Majalisar a ranar 30 ga Yuni, ya zargi ‘yan majalisar da kokarin yin sama da faɗi da shirin daukar ma’aikatan
Bayan Sa-in-sa data gudana a tsakanin bangarori biyun, har Shugaban Majalisar zartarwa Ahmad Lawan ya bada umarnin dakatar da shirin.
Ko da yake, Keyamo ya shaida wa wakilinmu a ranar Talata cewa, Kwamitocin zaɓin na jihohi, suna ci gaba da shirin kamar yadda shirin yake, biyo bayan sabon umarnin shugaban kasa, Buhari.
Ya ce: “Ina da umarni daga Shugaban kasa, ya ce in cigaba.
Mutane Milyan 4.48 Sun Nemi Aikin N-Power cinkin kwanaki 16 
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/mutane-milyan-448-sun-nemi-aikin-n.html

kwamitocin zaɓi na jihohi suna ci gaba da aiwatar da shirinsu. Babu wani abu da ya hana su cigaba da aiwatar da aikinsu tun farko.
“Za mu yi aiki tukuru don isar da aikin akan lokaci, amma idan akwai bukatar
canji za mu sanar da Shugaban kasa.”
An tsara Shirin ne don ɗaukar ma’aikata 1000 a kowanne yanki na kananan hukumomi 774 da ake dasu a kasar nan.
Ana sa ran aikin zai tanadi Naira Biliyan 52, don biyan wadanda suka samu damar shiga cikin shirin. 
Naira Dubu 20,000 ne za a dinga biyansu har tsawon wata uku. Ana sa ran aikin zai fara a watan Oktoba.
Nasir Ladan Argungu, shine shugaban kwamitin mutum 20, dake kowacce jiha, Sannan shugaban hukumar Ma’aikatar daukar ma’aikata (NDE) Keyamo ke kula da shirin.

Sabbin mutane miliyan 71 za su shiga ƙangin talauci  -Inji MDD
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/sabbin-mutane-miliyan-71-za-su-shiga.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.