Magu ya yi manyan Bayanai Bayan Sakinsa

Abubuwa 4 masu muhimmanci da Magu ya faɗi bayan sakinsa

 Bayan ya kwashe kimanin kwanaki 10 a tsare, Ibrahim Magu ya samu yan cinsa a yammacin ranar Laraba, 15 ga watan Yuli. 
Jim kadan bayan sakinsa dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ya zanta da jaridar The Nation. 
Legit.ng ta zakulo wasu muhimman abubuwa hudu da tsohon shugaban na EFCC ya fadi a jawabinsa. 

1. Zargin da ake masa duk marasa tushe ne Magu ya ce yayi matukar mamaki da ya karanta jerin zargin da ake masa, wadanda ya bayyana a matsayin marasa tushe. Kamar yadda yace, an hada jerin zargin ne don a ɓata masa suna da na EFCC.

Za A Riƙa Dandaƙe Masu Fyaɗe A Kano https://www.arewagist.com.ng/2020/07/za-rika-dandae-masu-fyade-kano.html


2. Kura ta ci kura:
 Magu ya ce abinda ya faru da shi shine ake kira da “kura ta ci kura”.

 Sai dai kuma ya dauki hakan a matsayin daya daga cikin haɗarurrukan da ke tattare da aikin nasa. 
3. Za a iya nasara da yaki da rashawa:
Dakataccen shugaban hukumar EFCC ya ce komai ƙalubalen da zai fuskanta, ya yarda cewa za a yi nasara a yaki da rashawa.

 A don haka yayi kira ga ‘yan Najeriya da su bada goyon baya a kan yaki da rashawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa gaba. 

4. Bai girgiza da abinda ya faru da shi ba: yace yana farin cikin sakinsa da aka yi.
 Magu ya ce wannan abun da ya faru da shi ba shi ake yaƙa ba, rashawa ake yaka.
 “Ina farin ciki da fitowata kuma na yarda akwai nasara.” 
A halin da ake ciki, fadar shugaban kasa Muhammadu ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa shugaban kasa ba zai samu rashin kwarin guiwa ba, a kan yaki da rashawa da yake yi.
 Ya bayyana hakan ne saboda kalubalantar sa da abokan hamayya ke yi.
 Ya ce ya riga ya shirya ganin bayan rashawa a kasar nan. 
Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu, wanda ya sanar da wannan matsayar ya yin zantawa da manema labaran gidan gwamnati a Abuja.
 Ya yi martani ne ga jam’iyyar PDP bayan fara bincikar Ibrahim Magu. Ya ce yanayin gwagwarmaya da shugaban kasar ke yi da kuma yaki da rashawa ya nuna yanayin abinda PDP ta bari bayan kammala wa’adin mulkinta.
 Shehu ya ce rashawa ta zama tamkar ba laifi ba ga PDP, lamarin da yasa suka kasa bambamcewa tsakanin rashawa da sata.

Buhari ya Bada Umarnin ci Gaba da ɗaukar Ma’aikata 774,000 
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/buhari-ya-nada-umarnin.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.