FG ta kaddamar da shirin bada tallafin N5,000 ga mutane 130,764 a jihar Zamfara

CCT: Mutane 130,764 a jihar Zamfara zasu amfana da tallafin N5,000 daga FG

– FG ta kaddamar da shirin bada tallafin N5,000 ga mutane 130,764 a jihar Zamfara

– Wadanda zasu ci gajiyar tallafin sun fito daga kananan hukumomi 6 na jihar kuma suna cikin rejistar shirin tallafawa ‘yan kasuwa

– Haka zalika, gwamnati ta jaddada aniyarta na kawo karshen ta’addanci a jihar Zamfara dama jihohin da ke fama da matsalar ‘yan ta’adda

Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar jin kai da bada tallafi ta kasa ta kaddamar da shirin bada tallafin N5,000 ga mutane 130,764 a jihar Zamfara.

Mutanen da zasu ci gajiyar tallafin shirin na CCT sun fito ne daga kananan hukumomi 6 na jihar, wadanda suka shiga cikin rejistar shirin tallafawa ‘yan kasuwa GEEF, na jihar.

A cewar Sadiya Umar Farouq, shirin CCT na a cikin bishiyar shirin samar da walwala na kasa NSIP, da aka kaddamar a 2016 karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Buhari ya Bada Umarnin ci Gaba da ɗaukar Ma’aikata 774,000 
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/buhari-ya-nada-umarnin.html

An samar da shirin da nufin tsamo talaka daga kangin talauci ta hanyar bada tallafin N5,000 a kowanne wata, ga wadanda ake kallo a matsayin mafi talauci a cikin al’umma.

Ta bukaci wadanda zasu ci gajiyar shirin da suyi amfani da wannan tallafi wajen bunkasa kasuwancinsu.

Ministar a madadin gwamnatin tarayya ta jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Zamfara na asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi a jihar sakamakon harin ‘yan ta’adda

Ta roki al’ummar jihar da su baiwa gwamnatin tarayya goyon baya wajen kawo karshen irin wannan kashe-kashen wulakancin da ake yi.

Sadiya ta tabbatarwa jihar cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin duk mai yiyuwa wajen ganin ta kawo karshen ‘yan ta’adda a jihar Zamfara da sauran jihohin da abun ya shafa.

Ta ce nan bada jimawa ba, kowa zai koma gudanar da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar hare haren ‘yan ta’adda ba.

Mutane Milyan 4.48 Sun Nemi Aikin N-Power cinkin kwanaki 16
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/mutane-milyan-448-sun-nemi-aikin-n.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.