Magu ya Ɓara Kan Zarge-Zargen da ake Masa

Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya yi magana game da jita-jitar da ke yawo a kansa

– An zargin Magu da ba Mataimakin shugaban kasa da wasu mutane Biliyoyin Nairori, wanda tuni tsohon shugaban hukumar EFCC ya karyata wannan zargi ta bakin wani Lauyansa

Kusan sa’a 24 bayan samun sakinsa, Ibrahim Magu ya rubuta takarda ga kwamitin shugaban kasa da ke binciken zargin badaƙala a EFCC, inda ya kare kansa.

Gidan talabijin na Channels TV ya bada rahoton cewa tsohon shugaban hukumar EFCC, ya rubuta takardarsa ne zuwa ga shugaban kwamitin bincike, Ayo Salami.

Abubuwa 4 masu muhimmanci da Magu ya faɗi bayan sakinsa
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/abubuwa-4-masu-muhimmanci-da-magu-ya.html

Ibrahim Magu ta bakin lauyansa, Wahab Shittu ya bayyana zargin cewa ya wa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Naira biliyan 4 a matsayin ƙarya.

Haka zalika shugaban na EFCC da aka dakatar ya ce babu gaskiya a maganar da ke yawo cewa ya biya fitaccen lauyan nan Femi Falana SAN, Naira miliyan 28.

Lauyan ya bayyana cewa wadannan duk labaran karya ne da ake yaɗawa domin a ɓata sunan mataimakin shugaban ƙasa, Ibrahim Magu da kuma Femi Falana.

Ta bakin Shittu, Magu ya musanta zargin yana da alaka da wani ‘dan kasuwar canji a Kaduna.


Za A Riƙa Dandaƙe Masu Fyaɗe A Kanohttps://www.arewagist.com.ng/2020/07/za-rika-dandae-masu-fyade-kano.html

A na su ɓangaren, tuni mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Femi Falana suka musanta zargin karɓar wasu kuɗi daga shugaban hukumar EFCC.

Game da gidansa da aka shiga akayi bincike a ranar 6 ga watan Yuli, Magu ya haƙiƙance a kan cewa babu wani abin zargi da aka samu a cikin gidan.

Ko da kayan alatu, ko daloli da agogo ba a samu a gidan ba. Lauyan ya ce binciken gidan bai sa an samu wasu hujjoji a kan tsohon shugaban hukumar na EFCC ba.

Bugu da kari, Wahab Shittu ya bayyana cewa motocin da aka cire daga gidan, wadanda hukumar ta ba Magu ne a matsayinsa na muƙaddashin shugaba.

Sai dai Lauyan ya koka da cewa ba su samu takardar zargin da ake tuhumar mai gidansa da su ba. Ya ce da zarar sun samu, Magu zai wanke kansa, kuma ya bukaci ayi adalci a binciken.

Osinbajo ya shigar da ƙarar wanda yayi masa Ƙazafin ya karɓi BIlyan 4 a gurin Magu
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/osinbajo-ya-shigar-da-ara-kan-yi-masa.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.