Majalisar NSCIA ta jinjinawa CBN kan kawo shirin bayar da rance mara kuɗin Ruwa

Majalisar NSCIA ta jinjinawa CBN kan kawo shirin bayar da rance mara kuɗin Ruwa

– NSCIA ta ce mafi akasarin Musulmai zasu gwammace ci gaba da zama a cikin talauci da dai su fuskanci ubangijinsu da laifin cin bashi mai kuɗin ruwa ba.
– Majalisar ta roki CBN da ta samar da tsarin karɓar bashin cikin sauƙi ta yadda talaka fitik zai amfana daga shirin.
Majalisar ƙoli ta gudanar da harkokin Musulunci ta Nigeria (NSCIA) ta yabawa babban bankin Nigeria (CBN) bisa kokarinsa na kawo shirye shiryen bayar da rancen da ba a biyan kuɗin ruwa.
Wata sanarwa daga cibiyar NSCIA, karkashin jagorancin, Sa’ad Abubakar, Sarkin Musulmi, ta ce shirye shiryen da ba kuɗin ruwa sun haɗa da shirin ‘Anchor Borrowers Programme’ (ABP).
Akwai kuma shirin bayar da rance don bunƙasa masana’antu CIFI, Shirin bada rance ga kananu da matsakaitan ‘yan kasuwa MSMEDF.
Da kuma shirin bada rance don bunƙasa manyan masana’antu RSSF, da kuma shirin bayar da rance don bunƙasa fannin kiwon lafiya.
Sanarwar, mai ɗauke da sa hannun mataimakin shugaba, Salisu Shehu, ta yi nuni da cewa cibiyar tana kallon ci gaban a matsayin hanyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.
Cibiyar NSCIA ta ce babban bankin Nigeria CBN ya saki wasu jadawalin ƙa’idoji da mutane zasu bi domin samun rancen kuɗaɗe ba tare da sun biya da kuɗin ruwa ba.
Yayin da take addu’ar tabbatar da tsare tsaren, NSCIA ta kuma jinjinawa CBN da gwamnatin tarayya na cimma irin wannan nasarar.
“Sama da shekaru masu yawa, ‘yan Nigeria Musulmai sun kasance koma baya a bangaren bayar da rance saboda gudun kudin ruwan da ake sanyawa kusan kowanne shiri” .
“Dole Musulmai su kaucewa kuɗin ruwa, haka zalika mafi akasarin Musulmai zasu gwammace ci gaba da zama a talauci da dai su fuskanci ubangijinsu da laifin cin kudin ruwa.
“Amma a bashin da babu kuɗin ruwa, to tabbas Musulmai zasu ci gajiyar ire iren waɗannan shirye shiryen, kusan kaso 60 ne zasu amfana.
“Abun lura a nan shine, idan bankin CBN ya samar da shirin, hakan zai ba bankin damar cimma ƙudirin kaso 80 na masu cin moriyar shirye shiryen bankin a 2020.”
Cibiyar NSCIA ta buƙaci bankin CBN da yayi amfani da dukkanin hukumomi da kafofin watsa labarai don samun sanar shirye shiryen.
Da tallafin hukumar wayar da kai ta kasa, da shirye shiryen talabijin da rediyo, za a wayar da kan al’umma da kuma yadda za subi don cin gajiyar shirin.
“Ya kamata ace an samar da tsarin karɓar bashin cikin sauƙi ta yadda talaka fitik zai amfana daga shirin,” a cewarta

Buhari ya Bada Umarnin ci Gaba da ɗaukar Ma’aikata 774,000 
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/buhari-ya-nada-umarnin.html?m=1

Leave a Reply

Your email address will not be published.