Anyi zanga-zanga saboda rusau a Kasuwannin Kano
Ƴan tireda a kasuwar Sabongari sun nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira a matsayin zalunci yayin da Hukumar Kula da Sufuri ta Kano KAROTA ta rushe musu rumfuna da shaguna.
Kwanaki uku da suka gabata ne Hukumar KAROTA ta yi rusau a wasu manyan kasuwanni na jihar Kano inda ta rushe fiye da shaguna 500 da ke wuraren da suka saɓa ƙa’ida a kan tituna.
A yau Litinin, ƴan kasuwa da wasu al’ummar gari suka yi zanga-zanga ta nuna bacin rai dangane da wannan lamari da wasunsu ke kira a matsayin toshe musu hanyar cin abinci.
A wani faifan bidiyo da jaridar Daily Trust ta wallafa a shafinta na Twitter, ya hasko yadda wasu matasa ke zanga-zanga a bakin Kasuwar Singer daura da Kasuwar Sabon Gari.
Rahotanni sun bayyana cewa, an yi ɗan takaitaccen rikici tsakanin jami’an ‘yan sanda da kuma wasu daga masu kasa kaya a gefen tituna a bakin kasuwar Sabon Gari.
Taƙaddamar ta auku ne a yayin da ‘yan kasuwar ke gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadin matakin da Gwamnatin Kano ta ɗauka na haramta kasa kaya a gefen titin kasuwar.
Shugaban hukumar NDDC ya Suma ya yin amsa tambayoyi
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/shugaban-hukumar-nddc-ya-suma-ya-yin.html?m=1
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/shugaban-hukumar-nddc-ya-suma-ya-yin.html?m=1
Kwanaki uku da suka gabata ne gidan Rediyon Freedom ya ruwaito cewa, Hukumar KAROTA ta sanar da kammala duk wani shiri na kai simame wuraren da ‘yan kasuwa ke kasa a kan tituna da wuraren da basu dace ba.
Shugaban Hukumar KAROTA, Alhaji Baffa Babba Dan Agundi, shi ne ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyarar gani da ido wuraren da aiki zai biyo takansu tun a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli.
A yayin da yake zantawa da manema labarai, Dan Agundi ya ce akwai fiye da shaguna dubu biyar da aka bari kara zube a gefen tituna da bakin kasuwanni a birnin Kano da kewaye.
Daga cikin kasuwannin da shugaban KAROTA ya wassafa sun haɗar da ta Sabuwar Tasha, Kwanar Ungogo, Unguwar Nassarawa, Yankin Masana’antu da kuma ta Sabon Gari.