Shugaban hukumar NDDC ya Suma ya yin amsa tambayoyi

Shugaban hukumar raya yankin Neja Delta ta NDDC a Najeriya ya shiga wani yanayi da ake ganin kamar suma ya yi a daidai lokacin da yake fuskantar wani kwamiti da ke binciken almubazarrancin da ake zargin hukumarsa da yi.

Yau ce rana ta hudu na zaman da kwamitin na mambobin majalisar wakilai ke yi yayin da take bincike kan wasu kudaden hukumar.

An shafe kusan sa’a daya ana yi wa Prof. Kemembradikumo Pondei tambayoyi kafin daga bisani aka fahimci cewa ba ya cikin hayyacinsa a kujerar da yake zaune kamar yadda kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito.

Wani hoton bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda Prof. Pondie sanye da wata riga mai launin shuɗi da ratsin fari ya tintsire ta gefen hannunsa na hagu, yayin da yake gaban kwamitin.

Mutane na hango shi suka zo cikin gaggawa domin taimakonsa, lamarin da ya janyo hatsaniya a zauren majalisar.

A cikin faifan bidiyon da ke ta yawo, an ga yadda wani mutum ya yi ƙoƙarin buɗe bakin Pondei yayin da wasu suka yi ƙoƙarin fitar da shi.

Mutane na zargin cewa mutuwar ɓangaren jiki ce da ake kira “stroke” ta same shi. An dai fitar da shi daga dakin taron yayin da kwamitin ya ɗauki hutun sa’o’i kaɗan.

Bayan nan kwamitin ya ci gaba da zaman da yake yi bayan zuwa hutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.