Majalisar dattawa ta buƙaci Shugabannin tsaron Najeriya su yi Murabus

Majalisa ta bukaci Buratai da sauran shugabannin tsaro su yi murabus

Majalisar Dattawa a ranar Talata ta buƙaci shugabannin hukumomin tsaro na ƙasar nan su sauka daga muƙamansu saboda cigaba da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar.

Majalisar ta cimma wannan matsaya ne bayan Sanata Ali Ndume, (APC, Borno) ya gabatar da ƙudirin nuna damuwarsa kan rahoton murabus ɗin da sojoji fiye da 200 sukayi.

Majalisar ta kuma buƙaci kwamitin ta na tsaro ya binciko dalilin da yasa jami’an sojojin suke yin murabus da kansu.

A jawabinsa, Lawan ya ce duk da cewa Rundunar Sojojin tana iya ƙoƙarin ta don samar da tsaro, ƙoƙarin nata bai wadatar ba.

Ƴan sanda sunyi Ram da masu garkuwa da mutane 33, da ƴan fashi 10
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/yan-sanda-sun-damke-gaggan-masu-garkuwa.html?m=1

Yan majalisar da suka tofa albarkacinsu a kan kudirin da Ndume ya gabatar sun koka kan yadda lamuran tsaro ke cigaba da tabarbarewa da kuma rashin iya gudanar da ayyukan cigaba a yankunan.
Sun ce jamian sojoji da dama suna tsoron rasa rayyukansu yayin yaki da ta’adancin hakan yasa suke barin aikin da kansu.
Mataimakin kwamitin kwastam, Sanata Ayo Fadahunsi ya bayar da shawarar shugabanin tsaron su yi murabus inda Sanata Betty Apiafi ta goyi biayansa.
Shugaban Majalisar, Ahmad Lawan shima ya amince da bukatar kuma sanatoci da dama da suka hallarci zaman suma sun amince.
Ahmad Lawan ya ce duk da cewa Rundunar Sojojin tana iya ƙoƙarin ta don samar da tsaro, ƙoƙarin nata bai wadatar ba saboda haka ya yi kira ga Shugaba Buhari ya naɗa sabbi.

Akpabio ya yi fallasa, ya bayyana wadanda aka bai wa kwangila
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/akpabio-ya-fallasa-waanda-aka-bai-wa.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.