Ƴan sanda sun kama matasan da suka kashe Matar Aure bayan sun yi mata fyaɗe

Ƴan sanda sun kama matasan da suka kashe Matar Aure bayan sun yi mata fyaɗe

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina a Najeriya ta ce ta kama wasu mutane biyu da ta jima tana nema kan zarginsu da yi wa wata matar aure fyaɗe, suka kuma koma suka kashe ta daga bisani, da za ta tona su.
Lamarin dai ya faru ne a watan Mayu a wani kauye da ke karamar hukumar Bakori ta jihar.
Rundunar ta bayyana damke mutanen ne kwana daya bayan wata nasarar da ta ce ta yi kuma ta kama wani mutum mai shekara 51 da ake zargi da lalata kananan yara mata ciki har da mai shekara hudu.
Kakakin rundunar ‘yansandan ta jihar Katsina, SP Gambo Isa wanda ya tabbatarwa da BBC ya ce za su ci gaba da aiki domin ganin an kawo karshen aikata miyagun laifuka a jihar.
A cikin ‘yan watannin nan an samu karuwar masu aikata fyade da lalata kananan yara a arewacin Najeriya.

Yan sanda sun damke gaggan masu garkuwa da mutane 33 da ‘yan fashi da makami 10 a jihar Adamawa

https://www.arewagist.com.ng/2020/07/yan-sanda-sun-damke-gaggan-masu-garkuwa.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.