Alƙali ya bada umarnin a kamo Shugaban hukumar HISBAH da wani Jami’in shari’a

Alƙali ya bada umarnin a kamo Shugaban hukumar HISBAH da wani Jami’in shari’a

Jaridar Daily Trust ta rawaito kotun shari’a da ke zama a garin Tudun Wada, karamar hukumar Sokoto ta kudu, ta bada umarnin cafke shugaban hukumar Hisbah na jihar Sokoto.

Alkali kotun shari’an ya bada damar kama shugaban HISBAH da Alkalin hukumar na reshen Sokoto ne a dalilin kin amsa gayyatar da aka yi masu a gaban kotu.

Rahoton ya bayyana cewa ana zargin jami’an biyu da laifin tsare mutane ba tare da bin doka ba. Sauran zargin da ke kansu suna da alaka da rikicin aure da cin mutunci da bata suna.

Ƴan sanda sun kama matasan da suka kashe Matar Aure bayan sun yi mata fyaɗe
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/an-sanda-sun-kama-matasan-da-suka-kashe.html?m=1
Caliphate Trust ta fahimci cewa wasu Bayin Allah; Hadiza Abubakar da Habibu Bawa ne su ka kai karar jami’an na HISBAH a kotu a dalilin wasu hukunci da hukumar ta yanke masu.

Hadiza Abubakar wanda ta rabu da mai gidanta ta zargi Alkalin hukumar da rashin gaskiya a dalilin mika ɗan da ta haifa zuwa ga mijinta, alhali yaron bai cika shekaru biyu ba.

Bayan haka Hadiza Abubakar tana karar Alkalin HISBAH da laifin ci mata mutunci da tsare ta na tsawon mako guda ba tare da wani dalili ba, wanda tace hakan keta mata alfarma ne.

Bazawarar ta shaidawa ‘yan jarida ta samu matsala da jami’an hukumar ne bayan sabani ya shiga tsakaninta da mai gidanta inda aka rufe ta har sai da tsohon mijinta ya nemi a bada belinta.

Bayan ta samu beli, HISBAH ta sake cafke ta, aka tsare ta na kwana biyu, sannan aka raba ta da ɗanta. Ta ce an ba ta N40, 000 a matsayin kudin shayarwa, wanda ta ki karba.

Yan sanda sun damke gaggan masu garkuwa da mutane 33 da ‘yan fashi da makami 10 a jihar Adamawa

https://www.arewagist.com.ng/2020/07/yan-sanda-sun-damke-gaggan-masu-garkuwa.html

Shi kuma a na sa ɓangaren, Habibu Bawa ya ce an tsare shi ba tare da hakki ba, kuma aka tursasa masa sakin mai dakinsa, sannan aka zarge shi da laifuffukan da bai san da su ba.

“Sun kira ni ofis cewa surukai na sun kawo kara ina zargin mata ta da aikata alfasha, don haka suka nemi takarda, sai Alƙalin hukumar ya buƙaci a biya ni N30, 000 in rubuta saki.” inji Bawa.

Da aka tuntubi shugaban HISBAH, Dr. Adamu Bello Kasarawa, ya ce sun daukaka ƙara zuwa babban kotu. Shi ma Alkakin hukumar, Ibrahim Rufa’i ya musanta zargin da ake yi masa.

Dalilan da yasa Goodluck yaje Fadar shugaban ƙasa 
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/dalilan-da-yasa-goodluck-yaje-fadar.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.