Buhari zai tafi ƙasar Mali Sasanta Rikici

Buhari zai tafi ƙasar Mali Sasanta Rikici

..

ASALIN HOTON,NIGERIA PRESIDENCY
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi Bamako babban birnin ƙasar Mali a ranar Alhamis.
Tafiyar ta shugaban ƙasar ta biyo bayan tattaunawarsa da Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda yana daga cikin masu shiga tsakani daga ƙunigyar ECOWAS da suka je Mali domin kawo sasanci.
Wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Yammacin Afrika irin su Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou sun amince su hadu a Mali domin tattaunawa don kawo sasanci tsakanin Shugaban Mali Boubacar Keita da kuma ‘yan adawa a ƙasar.
Ana sa ran Shugaban Ghana Nana Akufo Addo da kuma na Cote d’Ivoire Alassane Ouattara za su halarci tattaunawar.
Wannan ne karo na farko da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai fita daga Najeriya tun bayan da aka kulle iyakokin ƙasar sakamakon annobar cutar korona.
A baya dai ‘yan ƙasar na yawan ƙorafi dangane da tafiye tafiyen shugaban ƙasar.
Dalilan da yasa Goodluck yaje Fadar shugaban ƙasa https://www.arewagist.com.ng/2020/07/dalilan-da-yasa-goodluck-yaje-fadar.html
A ranar Litinin ne tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kai wa Shugaba Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja, inda suka tattauna a wata ganawar sirri.
Saƙon Twitter da Buhari ya wallafa ya nuna cewa Jonathan ya je Fadar Aso Rock Villa domin miƙa rahoton aikin sasanta rikicin siyasa ne wanda ƙungiyar ECOWAS ta tura shi ƙasar Mali a makon da ya gabata ga Buhari.
“Na karɓi rahoton wakilin ECOWAS na musamman a Mali, tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, game da rikicin siyasar Mali kuma za mu nemi shugaban ƙungiyar, Shugaban Nijar, ya yi mana cikakken bayani a matsayinsa na shugaba,” in ji Buhari.

Buhari ya amince da fitar da Naira Bilyan 75 domin tallafawa matasa 

Leave a Reply

Your email address will not be published.