Dalilan da yasa Goodluck yaje Fadar shugaban ƙasa

Goodluck Ebele Jonathan ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja, inda suka tattauna a wata ganawar sirri.

Saƙon Twitter da Buhari ya wallafa ya nuna cewa Jonathan ya je Fadar Aso Rock Villa domin miƙa rahoton aikin sasanta rikicin siyasa ne wanda ƙungiyar ECOWAS ta tura shi ƙasar Mali a makon da ya gabata ga Buhari.

“Na karɓi rahoton wakilin ECOWAS na musamman a Mali, tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, game da rikicin siyasar Mali kuma za mu nemi shugaban ƙungiyar, Shugaban Nijar, ya yi mana cikakken bayani a matsayinsa na shugaba,” in ji Buhari.

A jawabin da ya gabatar bayan ganawa da Buhari, Jonathan ya ce ƙungiyar haɓaka tattalin arzikin yankin Afirka Ta Yamma ba za ta taɓa goyon bayan tsige wani zaɓaɓɓen shugaba ba.

Tsohon shugaban yana magana ne kan kiraye-kirayen da ‘yan adawa suka riƙa yi ga Shugaban na Mali, Ibrahim Boubacar Keita da ya sauka daga muƙaminsa.

Goodluck Jonathan ya ce idan aka cire zaɓaɓɓen shugaba za a samu “rashin doka da oda a ƙasashe” sannan ya ce hatta AU – ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Afirka – ba za ta yi haka ba.

Buhari ya yi watsi da ƙudirin Majalisa Kan ya tsige hafsoshin tsaro
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/fadar-shugaban-kasa-ta-ce-shugaban-kasa.html?m=1

Leave a Reply

Your email address will not be published.