Magu ya fallasa waɗanda ya rabawa Gidaje da Motocin Sata

Magu ya yi raddi, ya bayyana ainihin waɗanda ya rabawa gidaje da motocin sata

Tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya ce wasu daga cikin motocin da ya karɓe daga hannun ɓarayi suna hannun ma’aikatun gwamnati da fadar shugaban kasa.

Ibrahim Magu ya bayyana cewa EFCC ta yi wa sabuwar ma’aikatar bada agaji da kuma fadar shugaban Najeriya, da hukumar FIRS da wasu ma’aikatu gwanjon motocin satan.

Jaridar Punch ta rawaito Magu yana cewa hukumar EFCC ba ta kammala karɓar kuɗin motocin daga hannun wasu ma’aikatun ba, amma an tsara yadda za a cire bashin daga kasonsu.

Mista Magu ya bayyana wannan ne a wata wasika mai taken ‘Re: Alleged Case of Conspiracy, Enrichment, Abuse of Public Office and Other Infractions’ da ya aikawa kwamitin Ayo Salami.

Muƙaddashin na EFCC wanda aka dakatar kwanaki ya wanke kansa daga zargin da kwamitin shugaban kasar yake yi masa na azurta kansa da kuɗi N550bn da dukiyar al’umma.

A martaninsa, Magu ya fayyace yadda har yanzu wasu motoci 450 da EFCC ta karbe daga hannun barayi suke zaune ba tare da an saida su ba duk da hukumar ta samu izni daga shugaban kasa.

Wadannan motoci suna garuruwan Abuja da Legas ne kamar yadda Ibrahim Magu ya bayyana. Akasin zargin da ake yi na cewa Magu ya rabawa na-kusa da shi motoci da gidaje.

Haka zalika a game da batun gidajen da EFCC ta karbe har abada daga barayin gwamnati, Magu ya ce an saidawa wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnati wadannan gidaje.

Daga cikin ma’aikatun da aka ba wadannan gidaje akwai: VON, sabuwar hukumar NEDC da aka kafa domin cigaban Arewa maso gabas, da kuma ma’aikatar fansho ta PTAD.

EFCC ta bada hayar gidajen da har yanzu ake kotu a kansu kafin a kammala shari’a. Wadanda suka karbi hayar gidajen sun hada da ma’ikatar kudi, sojojin Najeriya, FRC, NIDCOM, da FAAN.

Sauran ma’aikatun da su ka bukaci EFCC ta ba su hayar gidajen sata su ne; NHRC da NCAC kamar yadda Magu ya bayyana. Wasu gidajen kuma sun zama wurin killace masu COVID-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published.