Bayani tare da hotunan Otal na farko a duniya da aka yi masa fenti da ZINARE

Hotal na farko a duniya da aka kawata da zinari

  Otal na Dolce Hanoi Golden Lake da ke Vietnam an bayyana shi a matsayin otal na farko a duniya da aka yi wa fenti da zinari.


  Ba a dade da bude otal din ba don masu ziyara. 

An bayyana kayan alatun da ke cikinsa inda da yawa daga cikinsu aka kawata su da zinari. 


Daga cikin akwai kwamin wanka na zinari, masai na zinari da ababen cin abinci na zinari. 


 Babban otal din na nan a kusa da tafkin Giang Vo a tsakiyar garin Hanoi, babban birnin Vietnam. 


 An gano cewa otal din an malala masa zinarin bayan kwashe shekaru 11 da aka yi ana gininsa. 

Yana da dakuna 400 tare da bene mai hawa 25. 


Yana karkashin American Wyndham Hotels.

 An ware wasu dakuna na daban da ake bada hayarsu a farashin pam 5,200. 


A ranar wata Alhamis, yayin bude otal din, an nuna kwamin wanka tare da kofunan shan ruwa na zinari. An gano cewa a duk kwana daya ana biyan $250 yayin da ake bada hayar wasu dakuna $6,500. 


An gano cewa an yi amfani da $200 miliyan don gina otal din. 

Leave a Reply

Your email address will not be published.