Boko Haram sun yi wa Ma’aikatan Jin ƙai kisan wulaƙanci

Yadda Boko Haram suka kashe ma’aikatan kungiyar jinƙai biyar

A wani bidiyo da ke cike da tausayi Wanda kungiyar Boko Haram ta saki ranar Laraba, an Nuno yadda Suka kashe wasu Yan kungiyar Agaji biyar da suka Yi garkuwa da su.

A bidiyon, jagoran Boko Haram din yayi ‘yar gajeriwar huɗuba yana mai yin gargadi da mutane kada su riƙa aiki da waɗannan ƙungiyoyin Agaji da ke aiki a Kasar nan.

” Kuna gani dai basu damu da ku ba. Ko mun Yi garkuwa da ku, ba za su nemi fansar ku ba. Saboda haka ku sani wahalar banza kuke musu.

” Idan Kuma kuka ki jin wannan gargadi haka zamu rika bi muna dauke ku daya bayan daya muna kashe wa a duk inda kuke.

” Tuba zuwa ga Allah, hakan ne kawai Mafita.

Bayan haka sai shugaban Boko Haram din ya umarci daya daga Cikin matakan sa ya bude wa wadannan ma’aikata wuta nan take.

Da yake basu janye kyallen da suka rufe musu fuska da shi ba, bamu iya tantance  wadanda aka kashe din ba.

Hakan kuma mahukunta a Najeriya basu ce komai ba game da wannan kisa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.