Magu ya ƙalubalanci Malami ya kawo shaida guda daya tal inda ya karbi toshiyar baki

Magu ya ƙalubalanci Malami ya kawo shaida guda daya tal inda ya karbi toshiyar baki

Dakataccen Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya ƙalubalanci Ministan Shari’a Abubakar Malami ya kawo shaida ko da guda daya tal inda ya azurta kan sa da kadarar da ya ƙwato daga ɓarayin gwamnati, ko kuma shaidar ya karɓi toshiyar baki domin hana binciken wasu maɓarnata.

Magu ya yi wa Malami wannan fito-na-fito ne, yayin da yake amsa tambayoyin zargin azurta kai daga Kwamitin Bincike, sanadiyyar zargin da Minista Malami yayi masa.

Bayan damƙe Magu, ya shafe kwanaki 10 a tsare kafin a sake shi.

An riƙa kai shi Fadar Shugaban Kasa yana amsa tambayoyi a gaban mambobin Kwamitin Ayo Salami.

An riƙa fallasa zarge-zargen yin sata-ta-saci-sata da Malami yayi wa Magu.

Yadda EFCC ta yi wa Fadar Buhari da Ma’aikatun Gwamnati watandar wasu kayan da ta kwato daga hannun barayin gwamnati
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/yadda-efcc-ta-yi-wa-fadar-buhari-da.html

Yayin da Magu yake ƙaryata zarge-zargen da aka yi masa, shi ma ya karkato akalar sa, inda ya rika fallasa zargin rugumutsin harƙallar da ya Malami ya rika tabkawa.

PREMIUM TIMES HAUSA ts rawaito zargin da Magu yayi cewa Malami ne ya gurgunta kokarin da EFCC tayi domin dawo da tsohuwar Ministar Kudi, Deizani Allison-,Maduekwe domin ta fuskanci shari’a a Najeriya.

Sannan kuma Magu ya yi zargin cewa Malami ya bada odar yin gwanjon kayan sata ga wani kamfanin da ke gaban alkali ana tuhumar sa da satar danyen man Najeriya.

Magu har ila yau, ya yi zargin yadda wata kantamemiyar tankar jirgin ruwa dankare da danyen man fetur ta nutse a cikin aljihun Malami, aka yi ta lalube amma har yau ba a gano ta ba.

Magu ya fallasa Yadda Malami ya karya doka, yayi gwanjon kayan satar da EFCC ta kama

“Wadannan zarge-zargen karairayi da sharri da kazafi da ka ke min, abin tir ne domin muradin ka kawai ka bata min suna, ka zubar min da mutunci.

“Ina kalubakantar Malami da ke zargi na, ya kawo shaida ko da guda daya ce tal, inda na azurta kai na da kudade ko kadarorin da na kwato daga hannun barayin gwamnati. Ko kuma ya kawo ko da wuri daya wata shaida mai tabbatar da cewa na karbi toshiyar bakin hana a binciki wasu barayi ko mazambata.” Inji Magu.

Magu ya zargi Malami da cewa Kwamitin Binciken Kudaden Da EFCC ts Kwato, wanda Malami ya kafa a baya, bai yi masa adalci ba. Don ko sau daya baa bai wa shi Magu din damar kare kan sa ko sau daya ba.

Magu ya fallasa waɗanda ya rabawa Gidaje da Motocin Sata
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/magu-ya-fallasa-waanda-ya-rabawa-gidaje.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.