Majalisa na bincike kan zargin ɓacewar naira biliyan 100 a hukumar NEDC

Majalisa na bincike kan zargin ɓacewar naira biliyan 100 a hukumar NEDC

Majalisar Wakilan Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan zargin ɓacewar makudan kudaden da suka kai naira biliyan 100 daga Hukumar sake gina Yankin Arewa Maso Gabas da rikicin book haram ya daidaita.

Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Ndudi Elumelu ya gabatar da wannan zargin inda yake cewa kudin da aka baiwa kwamitin domin gudanar da aikin shafe ƙasa da shekara guda ba tare da ganin aikin da Hukumar tayi ba.

Elumelu ya zargi ministan kula da agajin gaggawa Sadiya Umar Faruk da hada baki da shugaban Hukumar Mohammed Goni, wajen kwashe naira biliyan 5 daga asusun Hukumar domin sayawa sojoji motoci ba tare da bin ka’ida ba.

Dan Majalisar yace akwai kuma zargin cewar shugaban Hukumar tare da wasu na kusa da shi, sunyi amfani da kudin Hukumar wajen sayan kadarori a unguwannin attajirai dake Abuja da Kaduna da Maiduguri ba tare da la’akari da kuncin rayuwar da mazauna yankin da rikicin book haram ya shafa ke ciki ba.

Elumelu ya kuma zargi shugaban Hukumar da kara kudin kwangila da biyan kwangilar da ba’a bayar ba, ko kuma raba kwangila guda ba tare da bin ka’idodin da aikin gwamnati ya tanada ba.

An hana Magu gabatar da daftarin hujjoji gaban kwamitinin bincike  https://www.arewagist.com.ng/2020/07/an-hana-magu-gabatar-da-daftarin.html

Shugaban gudanarwar Hukumar Mohammed Goni Alkali yayi watsi da zargin, inda yake cewa babu wani kudin da ya bata ko kuma akayi almubazzaranci da shi a Hukumar.

Alkali yace babu wanda ya baiwa Hukumar naira biliyan 100, kuma dangane da zargin kashe naira biliyan 5 wajen sayawa sojoji motocin aiki suna da rahoto kan abinda ya wakana, kuma kudin da suka kasha bai kai yadda ake zargi ba.

Ita dai wannan Hukuma ta raya Yankin Arewa Maso Gabas shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa ta a shekarar 2017 saboda ganin yadda rikicin boko haram ya daidaita Yankin, inda aka dora masa alhakin sake tsugunar da mutanen da rikicin ya raba da gidajen su da sake gina gidaje da makarantu da hanyoyin mota da wuraren kasuwanci.

Magu ya ƙalubalanci Malami ya kawo shaida guda daya tal inda ya karbi toshiyar baki https://www.arewagist.com.ng/2020/07/magu-ya-alubalanci-malami-ya-kawo.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.