Ƴan bindiga sun yi awon gaba da shanu 500 a Zamfara

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da shanu 500 a Zamfara

Mutane 9 sun jikkata a wani sumame da ‘yan bindiga suka kai wani kauye a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Rahotanni daga jihar Zamfara sun ce gungun ‘yan bindiga sun kai farmaki kan garin Wara-Wara dake karamar hukumar Tsafe, inda suka yi awon gaba da tarin dabbobi.

Ƙwaƙwƙwarar Majiyar ta sanar da Rediyon Faransa, cewar, maharan sun afkawa garin na Wara – Wara ne da maraicen jiya asabar haye kan babura akalla 15, inda suka kore dabbobi akalla 500.

Majiyar ta ce ba a samu asarar rai yayin harin ba, sai dai akalla mutane 9 sun jikkata, yayin da suke kokarin gudun tsira.

Jihar Zamfara dake arewa maso yammncin Najeriya na daga cikin jihohin da ke fama da hare haren ‘yan bindiga, barayin shanu da masu satar mutane don karbar kudin fansa.

A ɗauki mataki kan ma’aikatan agajin 5 da aka kashe a Borno – MDD
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/a-auki-mataki-kan-maaikatan-agajin-5-da.html?m=1

Leave a Reply

Your email address will not be published.