A ɗauki mataki kan ma’aikatan agajin 5 da aka kashe a Borno – MDD

A ɗauki mataki kan ma’aikatan agajin 5 da aka kashe a Borno – MDD

Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci gwamnatin Najeriya da ta ɗauki mataki kan kisan da ‘yan ƙungiyar ISWAP da ke iƙirarin jihadi suka yi wa wasu ma’aikatan agaji 5 a jihar Borno.

Sakatare Janar na majalisar Antonio Guterres ne ya yi kiran bayan da wani bidiyo wanda masu iƙirarin jihadi suka saki da ya nuna su, suna kashe ma’aikatan agaji huɗu da kuma wani jami’in tsaro.

An dai yi garkuwa da ma’aikatan ne tun a watan da ya gabata, sai dai a farkon wannan makon ne aka tabbatar da mutuwarsu.

Yankin arewa maso gabashin Najeriya ya shafe sama da shekaru goma yana fama da rikice-rikice masu alaƙa da masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram a ƙasar.

Sama da mutum 30,000 ne aka kashe a yankin tun bayan fara wannan rikici.

Magu ya fallasa Yadda Malami ya karya doka, yayi gwanjon kayan satar da EFCC ta kama

Leave a Reply

Your email address will not be published.