PDP ta buƙaci Buhari ya yi murabus saboda rashin tsaro

PDP ta buƙaci Buhari ya yi murabus saboda rashin tsaro

Babbar Jam’iyyar hamayya a Najeriya ta PDP ta buƙaci shugaba Buhari ya sauka daga muƙaminsa saboda yawan kashe-kashen da ake ci gaba da samu a ƙasar da kuma cin hanci da rashawar da suka dabaibaye harkokin gwamnatinsa.

Jam’iyyar wadda ta bayyana haka a taron manema labarai ta ce, gwamnatin Buhari ta ruɗe ta kuma rasa abin da za ta saka a gaba wajen yaƙi da Kungiyar Boko Haram da masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan bindigar da ke kashe jama’a ba  ji ba gani.

Shugaban Jam’iyyar Uche Secondus ya ce matsayar Majalisar Dattawa cewar shugabannin rundunonin sojin kasar su sauka daga mukamansu saboda gazawa wajen kare lafiyar jama’a, ya nuna cewar ɓangaren zartarwa ba ya aikin da ya rataya a kansa.

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da shanu 500 a Zamfara
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/an-bindiga-sun-yi-awon-gaba-da-shanu.html

Secondus ya ce tun lokacin da Kungiyar Transparency International ta bayyana cewar cin hanci da rashawa mafi muni na faruwa ne a karkashin wannan gwamnati, matsalar sai ci gaba da karuwa take yi, ganin yadda yanzu matsalar ta zama ado tsakanin jami’an gwamnati cikinsu har da hukumar da ke yaƙi da cin hancin.

Jam’iyyar PDP ta yi gargadin cewar Najeriya ta kama hanyar fadawa cikin matsalar tattalin arziki, kuma hakan na da nasaba da cin hancin da ke gudana a tsakanin jami’an gwamnati da ke rike da manyan muƙamai

Secondus ya ce abin takaici ne yadda ake sace kudaden da aka kwato daga hannun barayin gwamnati a gaban jama’a da kuma shugaban kasar da ke ikrarin yaki da cin hanci da rashawa.

Jam’iyyar ta ce abin da suke gani yau shi ne yadda Najeriya ta kama hanyar rugujewa saboda wadannan matsaloli da suka dabaibaye ta wanda ya zama wajibi shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayinsa na dattijo yayi jifa da kwallon mangoro domin ya huta da kuda wajen sauka daga mukaminsa.

An hana Magu gabatar da daftarin hujjoji gaban kwamitinin bincike https://www.arewagist.com.ng/2020/07/an-hana-magu-gabatar-da-daftarin.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.