Matawalle ya ƙaddamar da raba raguna 5,667 da shanu 993

Gwamna Matawalle ya raba raguna 5,667

da shanu 993

Gwamnatin jihar Zamfara ta fara raba raguna 5,667 da shanu 993 a matsayin tallafin babbar sallah ga jama’a daban-daban na fadin jihar.

Darakta janar na yada labarai da wayar da kai ga gwamnan jihar Zamfara, Yusuf Idris, ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Gusau a ranar Lahadi.
Bisa ga al’ada, gwamnatin jihar karkashin shugabancin Gwamna Bello Matawalle yana cika alkawarinsa na bada kayan tallafi da rage radadi ga jama’ar jihar.
“Abinda muka yi kenan da karamar sallah inda muka bada tallafi ga jama’a daban-daban musamman marayu da kuma marasa karfi har 100,000. Sun samu kayan sawa, kayayyakin abinci da kuma kudi don shagalin sallah bayan kammala azumi.
KU KARANTA KUMA: 
Ƴan bindiga sun yi awon gaba da shanu 500 a Zamfara
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/an-bindiga-sun-yi-awon-gaba-da-shanu.html
“A wannan lokacin, iyalai da kungiyoyi daban-daban sun samu kyautatawa na kayan abinci da kayan sa wa don shagalin bikin babbar sallah da ke zuwa a ranar 31 ga watan Yuli,” Idris yace.
Kamar yadda yace, an rarraba tallafin kayayyakin da wuri ta yadda za su amfana.
Kakakin gwamnan bai bayyana nawa aka yi amfani da shi wurin siyan raguna da shanun ba amma ya ce wadanda za su amfana sun kasance ma’aikatan gwamnati, kungiyoyi da sauransu.

NAPTIP ta cafke masu safarar mutane, ta ceto mutum 71 a jihar Kano
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/naptip-ta-cafke-masu-safarar-mutane-ta.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.