Ba za mu iya biyan ƴan N-Power biliyan 300 ba – Gwamnatin Najeriya

Wasu daga cikin ƴan Najeriya da suka ci gajiyar shirin N-Power sun yi zanga-zanga ranar Juma’a domin yin Allah-wadai da yunƙurin gwamnatin Najeriya na sallamar su daga aiki ta hanyar cire su daga cikin tsarin.

N-Power wani shiri ne da Gwamnatin  Najeriya ta ƙirƙira domin bai wa ƴan ƙasar da ba su da aikin yi aiki na wani lokaci, inda take biyan su naira 30,000 a wata.

A watan Yuni ne kuma ta ce za ta sallami waɗanda suke cikin shirin a yanzu domin sake ɗaukar wasu daban.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa masu zanga-zangar sun je ginin Majalisar Ƙasa da farko sannan suka wuce zuwa Sakatariyar Gwamnatin Tarayya dukkansu a Abuja.

Baya ga yin watsi da buƙatar gwamnati na raba gari da su, sun kuma buƙaci gwamnatin ta ɗauki mutum 500,000 da ke cikin shirin aiki sannnan ta biya su kuɗi N600,000 kowannensu.

Sai dai Ma’aikatar Jin Ƙai da Cigaban Al’umma – wadda ke gudanar da shirin – ta ce wannan ya saɓa wa alƙawarin da gwamnati tayi da su tun farko na cewa bayan shekara biyu za su ajiye ayyukansu.

“Bugu da ƙari, gwamnati ba za ta iya biyan naira biliyan 300 ba da suke buƙata ba,” a cewar Mataimakiyar Darakta a ma’aikatar Misis Rhoda Ishaku Iliya cikin wata sanarwa, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

“Gwamnati ba za ta iya cigaba da biyan ƴan N-Power ba har abada, saboda haka ne ma tuni aka fara shirin ɗibar wasu daban.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.