Boko Haram sun Kai wa Gwamnan Borno Hari

Yadda ƴan Boko Haram suka yi yunƙurin halaka gwamnan Borno
Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin najeriya ta tabbatar wa BBC cewa mayakan Boko Haram sun kai hari kan tawagar Gwamna Baba Gana Umara Zulum ranar Laraba.
Kakakin Gwamnan Malam Isa Gusau ya ce gwamnan ya tsallake rijiya da baya amma wasu ‘yan tawarsa ciki har da jami’in tsaro sun samu raunuka.
Ya ce gwamnan na kan hanyarsa ta zuwa garin Baga ne daga Monguno lokacin da mayaƙan Boko Haram suka kai wa ayarin motocin da yake ciki hari.
Boko Haram sun yi wa Ma’aikatan Jin ƙai kisan wulaƙanci
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/boko-haram-sun-yi-wa-maaikatan-jin-ai.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.