Akwai buƙatar jami’an tsaron Najeriya su tashi tsaye -Buhari

Akwai buƙatar jami’an tsaron Najeriya su tashi tsaye -Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a karon farko ya nuna cewa lalle akwai buƙatar ganin dakarun kasar sun ƙara tashi haiƙan wajen ƙoƙarin kare ƙasar daga matsalar tsaro da take ciki.

A wata hira da ba kasafai yake yi ba, Shugaba Buhari ya bayyana halin da ake ciki a yankin arewa maso yamma da kuma arewa maso tsakiyar ƙasar a matsayin abin tayar da hankali matuka.

“Ina yaƙinin cewa sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro daga rahotannin da nake samu ina tunanin za su iya ƙara tashi tsaye,” in ji kamfanin dillancin labarai na AFP

Buhari ya hau mulki ne shekara biyar da ta wuce, da alkawarin cewa zai murkushe ‘yan Boko Haram cikin dan kankanin lokaci, amma kuma har yanzu masu iƙirarin jihadin na ci-gaba da kai hare-hare musamman a yankin arewa maso gabashin kasar.

Bayan su kuma sai ga wasu matsalolin tsaron sun kunno kai suna kuma ƙara ƙamari, na rikicin ƙabilanci da ‘yan bindiga masu satar mutane don neman kuɗin fansa da kuma ɓarayin shanu, yawanci a arewacin kasar.

A cikin ‘yan kwanakin nan ne dai Majalisar Dattijan Najeriyar ta amince da wani ƙuduri da ke neman shugabannin rundunonin sojin ƙasar da suyi murabus, ko kuma a kore su sakamakon kara taɓarɓarewar matsalar tsaron

Leave a Reply

Your email address will not be published.