Gwamnan Zulum ya caccaki Sojoji kan Harin Baga

Harin tawagar Zulum: Gwamnan Borno ya huce fushinsa a kan dakarun soji

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Laraba ya nuna ɓacin ransa a kan yanayin aikin dakarun sojin da ke kokarin ganin bayan ƴan ta’addan Boko Haram a garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa ta jihar.

Ya nuna fushinsa a kan harin da wasu da ake zargin ƴan ta’addan Boko Haram ne suka kai masa a hanyarsa ta fita Baga.

Baga gari ne da ke da nisan a ƙalla kilo mita 196 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Gwamnan ya matukar fusata da lamarin, ganin cewa akwai dakarun sojin masu tarin yawa a nisan da bai wuce mil 4 ba wanda daidai yake da kilomita 4 daga Baga, amma basu iya kwace garin ba.

Zulum ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da sake buɗe babbar hanyar Monguno zuwa Baga ga ababen hawa wacce aka yi shekaru biyu da rufewa.

“Sama da shekara daya kuna nan, akwai soji 1,181 a nan. Idan ba za ku iya karɓar Baga ba wacce take da nisan da bai kai kilomita biyar ba daga inda kuke, toh me kuke yi?

Ina tunanin kawai mu hakura da Baga ko? Zan sanar da shugaban dakarun sojin da ya kwasheku ya kaiku inda za ku yi amfani.

“Kun ce babu Boko Haram a nan, toh su waye suka kawo mana farmaki? Ina tantama idan aka ce babu Boko Haram a nan garin,”gwamna Zulum ya tambaya.

Wasu waɗanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai wa tawagar gwamnan hari a garin Baga a ranar Laraba.

Ya jagoranci daruruwan jama’ar Kukawa, Cross da Baga zuwa tsohon garinsu bayan shekaru biyu da ‘yan ta’addan suka kwace garin.

Tun farko, kwamandan Operation Lafiya Dole da ke Baga, Birgediya Janar Garba, ya tabbatar wa da Zulum da tawagarsa cewa babu ‘yan ta’addan Boko Haram a garin.

Gwamnan wanda ya je zagayawa, ya koma Maiduguri lafiya. Kafin ya bar Monguno zuwa Baga, Zulum ya gabatar da motocin sintiri 12 ga dakarun sojin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.