Ganduje ya ƴanta firsunoni 43 Daga gidan yari

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya ziyarci gidan yari na Goron Dutse kamar yadda ya saba duk Sallah domin yanta firsunoni masu karamin  ya bilaifi.

Gwamnan ya ce Anyi la’akari da irin laifuffukan da Suka aikata da Kuma alamun sauyin halayen su, ya yin zaman su a gidan gyaran halin.

Gwamnan ya biya tarar su kuma ya bada izinin a sake su, sannan kowanne aka bashi 5,000 kudin mota domin komawa gida ga iyalin sa.

 Haka kuma an gabatarwa da Gwamna Ganduje wata mata mai suna Jennifer Okafor wadda a Karamar Sallah tana cikin mutum 300 da Gwamna yai wa afuwa sannan ya bada umarnin a dauke ta aiki a KAROTA wanda akai hakan, kuma a yanzu take maaikaciyar KAROTA.

Daga nan Gwamna Ganduje da tawagar sa sun ziyarci makabartar Dandolo domin gabatar da addu’o’i na musamman ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya. Da fatan Allah jikan su da rahama Ya kyautata namu zuwan.

Gwamna Ganduje na tare da Sanata Barau Jibrin da Sanata Kabiru Gaya da kakakin majalisar dokoki na jiha Rt Hon Abdulaziz Gafasa da Sakataren Gwamnati Alhaji Usman Alhaji da shugaban jam’iyar APC na jiha Hon Abdullahi Abbas da sauran manyan jami’an Gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published.